Tuesday 6 January 2026 - 00:45
Hukumar Birnin Rovigo ta Yi Fatali da Bukatar Gina Makabartar Musulmi

Hauza/Al'ummar musulmi a birnin Rovigo sun bukaci izinin gina makabartar musulmi mai zaman kanta tare da daukar nauyin dukkan kudaden da abin ya kama, amma hukumar birnin ta yi fatali da wannan bukata duk da cewa hakan ba zai taba asusun gwamnati ba. Wannan mataki ya haifar da tambayoyi masu karfi game da girmama 'yancin addini, mutuncin dan Adam, da kuma daidaito na gaskiya a kasar Italiya.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, wanda ya nakalto daga jaridar Corriere del Veneto: A birnin Rovigo dake arewacin Italiya, bukatar da musulmi suka gabatar wadda take a bayyane kuma ta bi dukkan ka'idojin shari'a, ta fuskanci tirjiya daga mahukuntan birnin.

Wakilan musulmi sun jaddada cewa wannan shiri ba zai zama nauyi ga gwamnati ba ta fuskar kudi, domin dukkan kudaden — tun daga sayen fili, fasalin gini, ginawa, har zuwa gudanarwa — al'ummar musulmi ne za su biya da kansu.

Abdulkabir Luzna, shugaban kungiyar "Solidale Senza Frontiere" a biranen Rovigo da Padova, ya jaddada cewa wannan bukata ba kawai batun addini ba ne, a’a, tana da alaka kai-tsaye da mutuncin dan Adam, girmama 'yancin gudanar da addini da amincewa da rarrabuwar al'adu a cikin al'ummar Italiya ta zamani kuma a cewarsa: "Gina makabartar musulmi ba wai kawai zai magance wata matsala ta zahiri ba ne, har ma wata amsa ce da ake bukata domin girmama al'adunmu da akidunmu."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha