A rahoton sashen fassarar Ofishin Yada Labaran Hauza, Sheikh Sanusi Abdulkadir, wakilin yan uwa Musulmi a Kano, a yayin wani jawabinsa ya jaddada matukar al'umma ba su kangarewa zalunci da azzalumai ba, ba ranar da wadannan masifofi da matsaloli za su kare.
A yayin jawabinsa ya bada misali na hankali ya ce:" Akwai abin mamaki ya zama mutane suna tunanin wadanda suke zaluntar su kuma su ne kuma za su cece su. Ta yaya mutumin da ba ya bada dukiyarsa ga barawo kuma zai sa ran cewa zai kare masa dukiya?"
Sheikh Abdulkadir ya kara da "cikakken hankali ba zai taba yarda ba cewa mutum zai bada jarinsa ga maha'inta sannan kuma yayi fatan ya same su salin alin.
Matakai Guda Biyar Na Gyara a Cikin Al'umma
Wakilin yan uwa Musulmin ya bayyana wasu matakai biyar da za a bi don yin gyara a cikin al'umma;
1. Matakin farko: Bara'a (tawaye)
Matakin farko shi ne bayyana tawaye da rashin bin zalunci da azzalumai.
2. Mataki na biyu: Wilaya
Wilaya ita ce sanin jagora da mai shiryarwa na gaskiya. Jerin shuwagabannin gaskiya daga Allah shi ne daga Manzon Allah zuwa Imamul Hujja (SA), kuma a wannan zamanin Sayyid Zakzaky (H) misali ne na wannan jagorancin.
3. Mataki na uku: Tsarkake Kai
Ya jaddada cewa ba yadda za a yi a iya gyara al'umma ba tare da an tsarkake kai ba. Da satar sawu daya na takalmi da kuma satar biliyoyin kudade daga baitul mali duk cikar su zunubai ne masu girma. Dole ne mutum ya nesanta kan sa daga haramun sannan ya lizimci duk abin da zai kusanta shi da Allah.
4. Mataki na Hudu: Addu'a
Sheikh Abdulkadir ya bayyana addu'a da komawa ga Allah a matsayin hanya mai muhimmanci da za a iya fita daga wannan bala'i.
5. Mataki Na Biyar: Wayar Da Kan Jama’a
Ya yi nuni da rashin sanin da yawa daga al'ummar game da zurfin matsalolin, ya jaddada wajibcin wa’azi, bayyanawa, wayar da kan jama’a, da bayyana rashin gamsuwa ta hanyoyin lumana. Ya kira wannan aikin a matsayin wajibi na shari’a.
A wani ɓangare na jawabinsa, Sheikh Sanusi Abdulqadir ya yi ishara da “Waki'ar Buhari” a ranar 12 ga Disamba, 2015, inda ya bayyana cikin tuhuma: “Ina sojojin da suke iƙirarin ƙarfi? Waɗanda suka kama mata, yara, har ma da jarirai, suna cewa an tsare musu hanya? Me yasa yanzu da ’yan ta’adda suka yi gida a cikin dazuzzuka, babu wannan ƙarfin?”
Da yake tunawa da rahotannin kafofin yada labarai, ya kara da cewa: “An tsara wannan aikin daga Isra’ila da Amurka, kuma Saudiyya ta biya kuɗin aiwatar da shi. Kakakin Yarima ya bayyana hakan yayin wata hira a Biritaniya, kuma kafofin yada labarai kamar sashen Hausa na Deutsche Welle (DW Hausa) sun ruwaito hakan.”
Sheikh Abdulkadir ya ci gaba da nuni da maganganun tsohon shugaban ƙasar Najeriya: “Buhari yana magana game da ‘wata gwamnati a cikin gwamnati’; alhali kuwa gwamnatin Boko Haram ta daɗe tana zaune a dajin Sambisa, shi kuma bai yi wani abu ba. A Sokoto da Zamfara ma, an kafa gwamnatin ’yan fashi, kuma aka yi shiru. Idan waɗannan ba misalan gwamnati cikin gwamnati ba ne to menene?.
Your Comment