Kamfanin dillancin labaran Hawza ya labarta cewa, Ayatullah Jawwadi Amoli ya yi magana kan muhimmancin tufafin malamai a cikin jawabinsa inda ya ce: “Wannan tufa ita ce tufatar Manzon Allah (saww), wajibi ne mu yi taka-tsan-tsan, da tsaftace ɗabi'un mu, domin abin da ya hau kan mu shi ne, isar da saƙon lafazi zuwa kunnuwan mutane, daga kunnuwa kuma zuwa zukata, ayyukanmu ne zai ingiza karantarwar mu zuwa gaba, har asamun ci gaba, ba ta hanyar maganganunmun mu ba; Idan muka rubuta littafi, mafi yawan abin da za mu iya yi shi ne mu isar da kalmomin zuwa idanuwan mutane domin su karanta su; amma daga gani zuwa fahimta, daga zahiri zuwa ciki, zamu ci gaba da kyawawan ayyukanmu da adalci ne -sabida mutane sun fi daukar karantarwa daga aiyukan mu- , mu san daraja da matsayin mu; muna son mu zama magada Annabawa, (asw), muna son mu zama ‘ya’yan Ali bin Abi Talib, (as) ne.
Labaran hauza/Ayatullah Jawwadi Amoli yana cewa: Wannan tufa ta Malanta ita ce rigar Manzon Allah (S.A.W), wajibi ne mu Malamai mu yi taka-tsan-tsan da tsaftace dabi'u, abin da ya hau kan mu shi ne isar da lafazin zuwa kunnuwan mutane, daga kunnuwa zuwa zukata kuma da aikin mu ne za'a samu ci gaba, ba da maganganun fatar bakin mu ba;
Your Comment