Sunday 22 February 2026 - 22:37
Sheikh Zakzaky Ya Ja Kunnen Malamai Kan Mayar da Tafsiri Filin Radde-radde

Hauza/ A daidai lokacin da ake gudanar da karatun tafsirin Alkur’ani mai girma a wannan wata na Ramadana, an yi kira ga malamai da masu tafsiri da su ji tsoron Allah, su guji mayar da mimbari wurin zage-zage, habaici, da kuma musayar yawu a tsakanin mutane masu bambancin ra’ayi.

A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, a cikin wani faifan bidiyo na baya-bayan nan, Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky (H), ya yi kira ga malamai da masu tafsirin Alkur’ani mai girma da su ji tsoron Allah, su guji mayar da mimbari wurin zage-zage, habaici, da kuma musayar yawu a tsakanin juna.

Sayyid Zakzaky ya nuna bacin ransa kan yadda wasu ke amfani da dandalin tafsiri wajen jafa’i da miyagun maganganu, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin girmama alfarmar littafin Allah da kuma watan Ramadana mai alfarma.

Hatsarin fassara Alkur’ani ba tare da ilimi ba

Sheikh Zakzaky ya jaddada cewa tafsirin Alkur’ani ba fagen wasa ba ne, domin mutum yana ƙoƙarin bayyana abin da Allah (T) yake nufi ne. Ya ba da misali da cewa, idan mutum ya yi kuskure wajen fassara maganar wani sarki, ya yi laifi babba, ballantana kuma fassara maganar Ubangijin talikai.

Jagoran ya ambato hadisin Manzon Allah (S) wanda ke cewa: "Duk wanda ya fassara Alkur'ani ba da ilimi ba, ko ya faɗi ra'ayinsa a cikinsa, to ya tanadi mazauninsa a wuta." Wannan na nuna cewa ba ra’ayin zuciya ake buƙata a tafsiri ba, sai dai abin da Allah yake nufi.

Sharadin kasancewa mai Tafsiri da "Ahaliyya"

Sheikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa ba kowa ne ya kamata ya yi tafsiri ba sai wanda yake da "Ahaliyya" (cancanta). Ya bayyana cewa:

Wanda ba shi da ilimin tafsiri, bai kamata ya tilasta kansa yin sa ba; gara ya koya ko ya saurari waɗanda suka sani.

Dole ne mai tafsiri ya kasance yana da babban laburaren littattafan magabata domin tuntuɓa, kamar su tafsirin Ma’athuri, Lugawiy, da sauran su.

Akwai buƙatar sanin ilimin "Ulumul Tafsir" wanda yake tamkar kimiyya ce mai zaman kanta.

‌Bin Tafarkin Maraji'ai a Fannin Tafsiri
Wani muhimmin batu da Sheikh Zakzaky ya tabo shi ne maganar "Taƙlidi a Tafsiri". Ya bayyana cewa kamar yadda mutum yake bin Marja’i a fannin fikihu, ya dace mutum ya kasance yana da malamin (Marja'i) da yake ruju’i gare shi a fannin ma’anonin Alkur’ani, maimakon faɗar abin da rai yake so kawai.

Kammalawa
A ƙarshen jawabin nasa, Sheikh Zakzaky ya yi kira ga al'umma da su kiyaye girmama Alkur’ani. Ya bayyana cewa mayar da tafsiri dandamalin zarge-zarge da radde-radde ba zai haifar wa al’umma komai ba sai rarraba kawuna da rashin albarkar karatun.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha