A cewar wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Hamid Melki, Mataimakin shugaban Hauzar Qom, ya bayyana hakan ne a wurin taron ma'aikatan hukumar gudanarwar Hauzar Qom, wanda aka gudanar a makarantar Imam Musa Kazim (A.S) domin bikin zagayowar nasarar Juyin Juya Hali.
Babban canji a tarihin Iran
Yayin taya murnar ranakun "Fajr", ya bayyana Juyin Juya Halin Musulunci a matsayin babban sauyi a tarihin zamani na Iran. Ya ce: "Juyin Juya Halin ya fitar da ƙasar daga yanayin cin hanci da rashawa, wulakanta addini, da matsin lamba na zamanin Dagutu, ya kaita ga daukaka, ruhaniya, 'yanci, da ikon bin dokokin Allah."
Tunatarwa akan kwanakin Allah (Ayyamullah)
Mataimakin shugaban Hauzar Qom ya yi nuni da wajibcin tunawa da manyan ayyukan Allah, inda ya ce: "Allah Madaukakin Sarki ya bukace mu da mu tuna da kwanakin Allah (Ayyamullah), kuma kwanakin Fajr na daga cikin manyan misalan wadannan kwanaki; kwanakin da suka fara tun daga 12 ga watan Bahman lokacin dawowar Imam Khomaini (R.A) har zuwa nasarar Juyin Juya Hali bayan kwanaki goma na gwagwarmayar al'umma."
Bambanci tsakanin zamanin jiya da yau
Hujjatul Islam Melki ya bayyana abubuwan da ya shaida a lokacin kuruciyarsa a shekarun 1978 da 1979, inda ya kwatanta yanayin zamantakewa da al'adu na mulkin Pahlavi. Ya kara da cewa: "A wancan lokacin, wuraren sayar da giya sun fi masallatai yawa a birane, kuma mutane ba su da damar kiyaye littattafan addini a gidajensu saboda tsoron jami'an tsaro. Amma a yau, kafafen yada labarai da cibiyoyin al'adu na Jamhuriyar Musulunci cike suke da ilimin Alkur'ani da na Ahlul Baiti (A.S), wanda wannan wata babbar ni'ima ce da ya kamata mu gode wa Allah akanta."
Jagora mai hangen nesa
Ya kuma yi nuni da cewa a yau ma Jamhuriyar Musulunci tana tsaye daram a gaban gaba daya zaluncin duniya da mulkin mallaka (Imperialism). Ya jaddada cewa: "A saman wannan fage na gaskiya, akwai babban masanin shari'a, jarumi kuma mai ilimi kamar Jagora (Ayatullah Khamenei), wanda yake jagorantar ƙasar da iko, hikima, da ruhaniya."
A karshe, Hujjatul Islam wal Muslimin Melki ya jaddada cewa yin aiki a cikin Hauza wani nauyi ne mai tsarki. Ya ce dukkan ma'aikata suna ƙarƙashin kulawar Imam Mahdi (A.J), don haka ya kamata su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da ikhlasi.
Your Comment