Monday 5 January 2026 - 15:04
Sayyida Zainab (AS) Ta Tabbatar Cewa Rainon Iyali da Isar da Sako Ba Sa Rabuwa

Hauza/ Namiji da mace daidai suke a wajen nauyin da ya rataya a wuyansu na addini da na dan Adam. Bayan faruwar yakin Ashura, dorewar yunkurin Karbala ya dogara ne ga ayyukan Sayyida Zainab (AS). Ya kamata al'ummar musulmi su tarbiyantar da mata masu ilimi da kwarewa wajen yin jawabi, bayar da amsoshi ga shubuhohi, da kuma fuskantar karkacewar al'adu.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, marigayi Allama Misbah Yazdi, a daya daga cikin jawabansa, ya taba tabo batun "Matsayin mace a cikin al'umma wajen kare addini", ga abin da yake cewa:

"Karbala za ta tsaya ne a Karbala idan ba don Zainab ba..."

Wasu na cewa aikin mace kawai shi ne kula da gida da tarbiyyar yara, kuma bai kamata ta shagaltu da wani abu daban ba.

Ba haka abin yake ba! Mace da namiji dukansu daya suke a mahangar dan Adamtaka, Musulunci, da kuma nauyin da ya rataya a kansu na tarbiyantar da wasu domin isar da ilimin Musulunci ga duniya.

Dukanmu mun san ayyukan da Sayyida Zainab (AS) ta gudanar bayan waki'ar Karbala. Nauyin kare labarin Ashura bayan shahadar Shugaban Shahidai (Imam Hussain AS) ya koma wuyan Sayyida Zainab ne. Idan ba don kokarin Sayyida Zainab (AS) ba, da ba mu san komai game da labarin Karbala ba. Dorewar wannan labari ya samu ne albarkacin kokarinta.

Shin mata muminai za su iya yin jawabi domin fuskantar bata da kauce hanya?

Idan har suna son su zama masu jawabi, su bayar da amsoshi ga shubuhohi, kuma su daka wa mutane irin su Yazidu da Ibn Ziyad dakuwa a baki (da hujjoji), shin tarbiyyar yara kadai ta isa? A ina ya kamata a tarbiyantar da su (don samun wadannan kwarewar)?

Ya kamata al'ummar Musulmi su kasance da damar samar da hakan. A yau kuna gani a duniya cewa mata ne ke da alhakin yawancin rashi da bala'o'in al'adu na duniya.

Waye ya kamata ya tsaya ya fuskance su? Su wane ne ya kamata su hana tsatso mai zuwa na juyin juya halinmu fadawa cikin wadannan barna?

Tarihin Jawabin: 31 ga Oktoba, 2019

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha