Kafar yada labarai ta Hauza ta ruwaito cewa, Wannnan wani bangare ne daga karshen Jawabin da Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ya gabatar ga dandazon dubban ‘yan’uwa Musulmi da suka halarci taron Yaumush Shuhada a ranar Asabar 25 ga watan Rajab, 1435, wanda yayi dai dai da (24/5/2014) a filin Polo dake kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah Zariya.
A ciki Shehin Malamin ya yi bayani dangane da makircin dake cikin kai hare-hare a kauyukan Zamfara, Birnin Gwari da sauran Garuruwa a Najeriya, Asha karatu lafiya.
Sabon Salon Mamayar Afirka
"...Kunga yanzu muna fuskantar wani abu a kasarnan. Dama can nasha wannan maganar cewa; akwai wani abu yananan tafe. A wa’azuzuka daban-daban na ambata wannan. To, Akwai wani abu na tafe, shi ne; mamayar Afrika. Wanda suka ce, sunyi nazari sunga cewa; karnin da za a shiga (tun kafin ma a shiga), tun kafin a shiga karnin nan. 2000 din nan. Tun a 1900 suke fada. Suka ce; karni na gaba, sunansa KARNIN AFRIKA.
Domin sunyi nazari sunga cewa, Afrika na da kusan kashi biyu bisa uku na dukkan dukiyan da ake dashi a duniya. Saboda haka za a sake kama Afrika na biyu. Sabon rububi. Abin da aka kira ‘scramble for Africa’. Suka ce za a yi ‘second scramble’. Za a yi sabon rububi. Saboda lokacin rububin Afrika na wancan karon. Tsakanin daulolin Turai da Ingila da Faransa da ‘Germany’ da ‘Italia’ da ‘Portugal’ da ‘Belgium’, duk kowanne, wannan ya kama nan, wannan ya kama nan, wannan ya kama…. Har suka je ‘Berlin, suka yi ‘conference’ aka raba. Kowa ya fadi inda ya kama aka tsaga aka ba, aka ce; kowa ga nasa. To, sunce za a yi wannan karon.
To, sai kuma Amerika ta zo ta ambata ta ce; zata yi amfani da ta’addanci wajen sake kama Afrika. To, shiyasa ku ga wannan abin da yake faruwan yanzu. Sunyi a Libya. Bayan lokacin da suka ji dagowar Larabawa din nan, da dagowar Misra, abin ya firgita su, suka ce, to, suma bari suyi na su. Sai suka yi a Libya. Suka je suka rugurguza Libya din, suka kashe Gaddafi. Yanzu bakomai dake gudana a Libya banda kashe-kashe da fada na Kabilanci. Tsakanin Melisha da kabila. Da na warin launi. Su ko suna diban dukiya.
Libya da Nijeriya suna da mai mai Dadi (Sweet Crude)
To, dama da Libya da Nijeriya ance su suke da mai din da ake ce mishi; mai zaki , mai zaki ‘sweet crude’. To, na Libya yanzu dama na su ne. Na Najeriya dama na su ne. Tunda suna samun gaulaye ne su ajiye. Kullum basu da wani aiki, sai dai su samo wani Gaula su ce shi ne shugaban kasa, su samo Dolo su ce shi ne Mataimakinsa, su sami Gabo su ce shi ne Gwamna, su samu Wofi su ce shi ne Minista, su sami, ga sunan. Su yi ta tatsan arziki din.
Salon Mamayar kasa
To, yanzu kuma sai suka zo da wani salon to, mamayan kasa. Saboda haka suka shirya suka mamaye Mali. Yanzu ko shekaranjiyan nan a labaru suna cewa; an fafata a Kidal da Gawo da wa’insu ‘yan bindiga. Haka kawai zasu bayyana a unguwa su yi ta zubar da wuta, bakasan wa ake harbi ba. A ce ai wasu ne masu kishin Islama ne suka bayyana ana fafatawa. Alhali Mali, Zinariya suka gano a Mali. Zinariyar da ba a san inda take ba tuntuni. Don dama ana da labarin akwai Zinare a Mali. Mansa Musan nan, wanda ya yi tafiya zuwa Hajji. Wanda ya shiga tarihi.
Wanda aka ce, ya tafi da Rakuma dubu dauke da kayan Zinare da Bayi dubu, kowanne yana dauke da Sandan Zinare. Da yaje Misra, Zinaren da yakai Misra sai da ya sauke farashin Zinare da har yanzu bai tashi ba. Da yaje Makkah ya yi gine-ginen da sai kwanannan ne Ali Saud suka rusa wasu. Suka rurrusa suna gine-ginen su a gewayen harami. Amma har ya zuwa dan shekarun baya gine ginen Mansa Musa abin kallo ne. To, Gwal din nan ba a san inda yake ba. Ansan akwai Gwal. A ina ne ma Mansa Musa ya yi fada, ba a sani ba. Ko su ce, NAWA ne, ko su ce Iraira, ko su ce kaza ne, Bil ne, a je Bil a shafa ba a gani ba. A ce wannan garin ne, a je ba za a gani ba.
To, yanzu sun gano Gwal din, saboda haka, suka tsara yadda suka mamaye Mali. Suka ce ‘yan kishin Musulunci ne suka fada daga Aljeriya. Ba dan Mali ko daya a cikinsu. Wai sun kama rabin Mali fiye ma da rabi, sun kafa daula wai sunanta ‘Azwat’. Sannan sai Faransa maza wuf ta shiga wai ta fatattake su. Ta riga Amerika shiga. Don Amerika ita ta shirya shiga. Sai suka… wai sun fatattake su. Bayan wannan, sai Faransa, akwai ‘Diamond’ a Central Africa, shi ne; sunje diban ‘Diamond’ ne sai suka hada fada. Wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba. Wai su Saleka, suka shiga cikin Central Africa Republic, suka yi ta kashe Kiristoci suna kona Cocina da sunan wai su Musulmi ne.
Sannan su ba ‘yan Central Africa Republic. Suka fita kasar. Bayan sun fita Afrika ta tsakiya, sannan sai suka kawwana Melisha na kirista wai su Anti Balaka. Sai suka bi suna kashe musulmin da suke zaune a kasar. Wai suna ramuwar gayya. To, inma wadancan Saleka sun zo sun kashe ku, ‘yan kasar ku ne? Daga wani wuri fa suka shigo, suka kuma fita. Waima su suka fara. Kamar yadda suka yi juyin mulki a Mali. Suka wani wai shi Sanogo ya zama shugaba. Wai shi ya yi juyin mulkin akan cewa, shi Sulaimanu Traore ya kasa ima ‘yan tawayen Arewa.
Sai kuma aka ce, ‘yan tawayen Arewa din ma sun kwace kasar gaba daya ma a karkashin shi Sanogo din. To, nan ma na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, sai aka ce, wai wani musulmi ya yi juyin mulki na soja. Wai sunanshi Michael Odofia. Kun taba jin sunan musulmi Michael? Wai Musulmi ne, amma sunanshi Michael Odofia. Wai Odofia Michael ya kwace mulki. Wai shi musulmi ne. Ya za a yi Musulmi ya zama shugaban kasar a inda mafi Yawa Kirista ne? Ashe haramun ne Kirista ya zama shugaban Kasa a kasan da yake mafi yawan su Musulmi ne, shi ne har aka samu Kiristoci suka zama shuwagabanni a Najeriya? Da wannan suka fake, suka je suka shiga cikin Central Africa suna ta kashe Musulmi musamman Fulani makiyaya wanda ba-su-ji-ba-ba-su-gani ba. Diamond suka je diba.
Kudancin Sudan da suka ga bazai yiwu sukai cewa; ‘yan kishin Isalama ba ne, sai suka hada fadan Kabila tsakanin Dinka da Nod. Amma shi ne, hana ma China Mai. Ya zama tunda dama Kudancin Sudan suna dasawa da China, ya zama basu tare da China. Najeriya kuwa, shi ne suka bullo da wani abu wai shi Boko haram. Wanda tuntuni su wasu ba’adin Amurkawa sun riga sun ambata sanannen abu ne cewa, ba wani abu wai shi Boko haram kikkiran Amerika ne.
Sace wasu 'yan mata awata Makarnta aikin Gwamnatin Janathan ce)
To, yanzu gashi wai Boko haram sun sace wasu ‘yan mata a wata Makaranta, amma su ‘yan matan da iyayensu sun san suwa suka sace su. Sun sani sarai, gwamnatin Jonathan ce. Ance ana ta zanga-zanga, na ce; wai ana zanga-zangar me ne? Harda jan kaya. Ina jan kayan ya fito? Wai ku bamu ‘yan matanmu. Wa zai baku? Jonathan ko Shekau? Idan Jonathan ne zai baku ‘yan matan ku, eh, to, ku yi mishi zanga-zanga ya fito da ‘yan matan inda yasan ya ajiye. Don yasan Barikin Sojan da ya ajiye su. Idan ko Shekau ne, kunsan a wacce Sheka yake? Yaushe yake jin ku? Yananan shima suna tsare da shi a wani Barikin Soja. Don kayan su ne duka.
Babu wata tsiya wai ita Boko Haram
Ba wata tsiya wai ita Boko Haram, karyar tsiya ce kawai. Wannan iskancin din bamu za a yiwa ba. Idan kuna so ku zo ku diba Mai ku diba zinariya ku diba arziki, ku zo a yi ciniki. Ko da cinikin ‘Mugabala’ ne. Mu baku Kwai ku bamu Kaza. Ko, mu baku Rakumi ku bamu Rago. Mun yadda gwara hakanan. Amma kwazo ku yi mana iskanci da addininmu. Ku ce mana muna fama da musulmi masu kishin addini kunzo ku cece mu. Alhali munsan kunzo ku cuce mu ne.
Ga Boko Haram sun Shigo na sosai
To, ga Boko haram din sun shigo na sosai, su ne; Amerika. Suna shigowa ko, yalai sai kashe-kashe. Sai tashe-tashen bama-bamai. To, kuma wannan irinshi fa suka yi a Afghanistan ko kuma suke yi har yanzu. Kuma irinshi suke yi har yanzu a Irak. A Afghanistan suna da filaye gomomi ne na filayen jirgin sama suna kwasar dukiyoyi. Da sunan suna yaki ne. Asali sun shiga da cewa; suna neman Bin Laden ne. Ba a san inda Bin Laden yake ba. Can kuma suka ce; Bin Laden dinma sun kashe shi a wani wuri ma ba a A
fghanistan din ba. To, suna menene a Afghanistan? Har yanzu sunanan. Irak ko suka shiga suka ce akwai WMD. Suka rugurguza Irak. Suna ta cewa; za a ga WMD din. Za a gani. Can sai kuma, har suka kamo Saddam ma, har cocila suka kunna suna kallon bakinsa, imma WMD din yana cikin bakin Saddam ne, Duk sun dudduba. Sai suka juya kuma wai suna kai musu Dimukradiya ne. Yanzu kuma sunce ba WMD amma basu bar Irak ba. Sunanan suna tatsar dukiya. Kullum sai tashe-tashen bama-bamai da kashe-kashe. Kuma su suke yi.
To, yanzu tunda suka shigo nan muma abin da suka yi mana shiri kenan. Haka kawai munyi gari abin da muke jin labari a wasu kasashe ya kunno mana bagtatan. Mun tabbatar ba wata kungiya wai ta kishin Islama wai wanda ake ce ma ta wai Boko Haram. Mun tabbatar bata. Ba ta da wujubi sam-sam. A ina? A wani gari? A wani titi? A wacce unguwa? Amma bama-bamai na tashi. Su suke sa bam-baman nan. Ko su haka rami wawukeke su saka su birne ko su matsa ‘remote’ ko su zo da Mota su ajiye su danna. Aikin kenan. Ko wasu su bayyana su bude wuta. Saboda mene? Dukiya suka zo di ba. A tsakanin Zamfara Zinare ke kwance, suna so su share Eriyan da Zinare yake ne, ya zama ba mutum ko kadan, su yi filin jirgin sama, su yi sansanin Soja su rika kwasan Zinariya. Nan tsakanin Zariya da Birnin Gwari, Zinare ne yake kwance da duwatsu masu daraja. So, suke su share mutanen wurin su kafa filin jirgin sama su kwasa. Tsakanin Sakwkwato har zuwa Borno, daga Uranium sai Zinare sai Platinum. Shi suka zo diba. To, ku zo mana ai ciniki. Ko da ma ku bamu Kaza mu baku Rakumi, amma ku barmu da ranmu kuma ku kyale mana addininmu.
Amma menene na cewa; zaku shigo ne, da yinma mutane wayayyu babarodo. Ina ku kuke da wayon? Yaushe aka yi Ba amurke? Yaushe aka yi Bature ma tukunna? Wani wayo yake dashi? Eh mana. Dauko tarihin Bature ka karanta mana, badaje, maye, dan bori! Yaushe ya waye harda zai mana wayo? Rashin kunyan banza kawai. Ku zo ai ciniki. Kuna da Bindiga mun sani, kun iya kisan kai, amma a kyale mana addininmu.
To, yanzu abin da ya kawo su kenan kuma yanzun musiban yana rutsawa nan da nan tsakanin ‘yan’uwa. Kunsan a Gwoza. Harma sun rutsa da garin Gwoza, sunce, baza su shiga ba, saboda suna jin tsoron ‘yan shi’a. Don akwai wani dan uwa da suka kama suka cire masa kai, suka fille kansa sosai, amma sai suka ji kalma, kan na Kalmar shahada. Suka duba ga Kai yana ‘la’ilaha illallah Muhammadur Rasulillah’ ga gangan jiki din.
To, shi ne suka ce; suna jin tsoron garin saboda ‘yan shi’a. To, wannan abin da muke fuskanta kenan. Kuma nasan sun riga sun ambata tuntuni, abin da suke jin tsoro kawai ita ce; wannan harka din. Don sunsan ita ce kawai zata taka musu burki.
Amma muna ma kira ga su wa’innan mutanen, mun ji an kira ka baka ci zabe ba ance kaine kake da mukami, mun ji baka cancanta ba, mun ji kai Gaula ne, ko Gabo ne ko Sakarai ne ko Shashasha ne, ko Wofi ne, to, mun ji kaine. Yanzu ko a hakanan ka yadda yanzu a baka kudi a kashe mutanenka? Kai baka da tunani? Shikenan an baka mukami an baka kudi shikenan a kashe mutanenka. Shirun ya isa ga al’umma. Kuma ba kyaleka za su yi ba, in sun gama dakai, in ka zama fanko kashe ka zasu yi, haka suke yi. Saddam din nan da suka kashe kayansu ne, Gaddafin da suka kashe kayansu ne, duk su suka yi su. Suka kama suka kawar da su. Kaima in sun gama dakai zasu yanka kane, an gama.
Nasan wannan, ah, munasabar yaumush shuhada muna da Magana da yawan gaske ganin cewa; wannan abin da ya kunno kai a kasarnan lallai fa ya shafe mu. Kuma lallai kam fuskantan wannan da duk iyan abin da muke iyawa, aiki ne ga addinin Musulunci. Kuma wanda duk suka kashe a cikinmu sunansa Shahidi! Bance muku tunda su suna daukan Bindiga ne, muma zamu dauki Bindiga ne, amma muna da makamai irin namu. To, su zamu dauka insha Allahu.
Allah Ta’ala muna rokonka ka nuna mana Yaumush Shuhada na badi cikin koshin lafiya da yalwar arziki. Allah madaukakin Sarki ka karemu da kariyarka, ka taimakemu da taimakonka ka dora mu birbishin makiya.
Wasallahu Ala Muhammadin wa’alihid dayyibinad dahirin. Wassalamu alaikum warahmatullahi.
Ciyar Wallafa aiyukan Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ce ta rubuta.
Your Comment