Monday 22 December 2025 - 02:39
Yahudawa Su Bar Isra'ila

Hauza/ Rabi (Babban Malamin Addinin Yahudanci) David Feldman, wanda yake mamba ne a ƙungiyar "Neturei Karta" mai adawa da sahayoniyanci, ya bayyana bambanci na asali tsakanin addinin Yahudanci da kuma tsarin sahayoniyanci (Zionism), yana mai jaddada cewa laifukan da ake aikatawa na tursasawa Falasɗinawa ba sa wakiltar addinin Yahudu.

Bisa rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, a daidai lokacin da ake samun kace-kace a duniya game da cakuda Yahudanci a matsayin wani addini Sahayoniyanci kuma a matsayin harkar siyasa, da kuma taurin kan gwamnatin mamayar Isra'ila na gabatar da kanta a matsayin "kasar da ke wakiltar Yahudawa" yayin da take ci gaba da kisan kiyashi, muryar wani malamin addinin Yahudu mai adawa da wannan ikirari ta fito fili.

Babban malamin Yahudawa, David Feldman, na ƙungiyar "Neturei Karta" mai adawa da sahayoniyanci, a yayin wata tattaunawa ta musamman da "Arabi 21" ya bayyana bambanci na asali tsakanin addinin Yahudanci da kuma tsarin sahayoniyanci, ya bayyana cewa laifukan da ake aikatawa akan Falasɗinawa ba ya wakiltar Yahudanci kuma cutarwa ce mai girma ga Yahudawa a duk fadin duniya.

Feldman, a cikin wani saƙo na kai tsaye zuwa ga matasan Yahudawa da ke cikin haramtacciyar ƙasar Isra'ila, ya yi kira gare su da su gudu su bar gwamnatin Yahudawan, yana mai gargadin cewa ci gaba da yaƙin kisan kiyashi ba wai kawai Palasdinawa da Musulmi yake wa barazana ba, har ma yana ninka haɗarin ƙiyayya da tashin hankali ga Yahudawa a ƙasashe daban-daban na duniya. Haka kuma ya bayyana ra’ayinsa game da batun samar da ƙasashe biyu (two-state solution) da aka dade ana tattaunawa akai. Wannan shine rubutun tattaunawar:

Tambaya: Da farko, gabatar da kanka da kuma ƙungiyar da kake cikinta?

Amsa: Sunana Rabi David Feldman, kuma ina tare da ƙungiyar "Neturei Karta" ta duniya. Mu ƙungiya ce ta addinin Yahudu ta duniya wadda ke ɗaga muryar dubun-dubatar Yahudawa a duniya wajen adawa da falsafar sahayoniyanci, da ƙasar Isra'ila, da kuma dukkan laifukan da ake aikatawa kan ƙasar Falasɗinu.

Tambaya: Menene ra'ayinka game da abin da yake faruwa a Falasɗinu?

Amsa: Abin da ke faruwa a Falasɗinu ba wai kawai babban laifi ba ne a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa da keta dukkan ƙa'idodin haƙƙin ɗan Adam, a'a, har ma a mahangar addinin Yahudu wannan babban laifi ne.

Kisa, sata, da zaluntar al'umma baki daya, duka waɗannan abubuwa ne da ba su da gurbin zama a koyarwar Yahudanci, musamman ma idan hakan yana faruwa ne a Falasɗinu. Waɗannan mutanen (Falasɗinawa) sune mutanen da suka girmama mu kuma muka daɗe muna rayuwa a ƙarƙashin kariyarsu na dogon lokaci, har zuwa shekarun 1920 lokacin da Sahayoniyanci ya shigo ƙasa mai tsarki.

Don haka, abin da yake faruwa kuskure ne, kuma muna ƙoƙarin taimaka wa mutane su fita daga tarkon farfagandar Sahayoniyanci domin su fahimci cewa yin adawa da waɗannan laifukan ba yana nufin cewa mai yin sukar mai ƙiyayya ga Yahudawa (antisemitic) ba ne.

Tambaya: Shin Isra'ila tana wakiltar dukkan Yahudawa ne a duniya?

Amsa: Gwamnatin Isra'ila ba ta wakiltar dukkan Yahudawa, kuma tabbas ba ta wakiltar addinin Yahudanci. Akwai adadi mai yawa na Yahudawa a sassan duniya daban-daban waɗanda ke adawa da waɗannan laifukan, kuma addinin Yahudanci ma yana adawa da dukkan waɗannan laifukan.

Mutane masu lamiri, masu gaskiya, da masu son adalci, dole ne su ɗaga muryoyinsu yayin da suke gani da idanunsu ana shekaru biyu ana kisan ƙiyashi wanda har yanzu ba a tsayar da shi ba.

Tambaya: Shin Yahudawa suna samun tasiri a abin da Isra'ila ke aikatawa a Falasɗinu, kuma ta yaya?

Amsa: Abin takaici, ana kashe mutane, yara suna mutuwa saboda yunwa, kuma abin bakin ciki hakan yana nan yana ci gaba. Dole ne mu yi duk abin da za mu iya domin sauya wannan yanayin, mu dakatar da wannan mamayar, mu tabbatar da adalci ga al'ummar Falasɗinu, sannan mu samar da tsaro ga mutanen Yahudu. Domin kuwa Yahudawa suna fuskantar sakamakon ƙiyayya da haɗari saboda abin da ake aikatawa da sunansu.

Muna tuhumar ƙungiyar sahayoniyanci da gwamnatin Isra'ila, ba wai kawai don aikata waɗannan gagaruman laifukan kan Falasɗinu ba, har ma don sanya rayuwar Yahudawa cikin haɗari, yayin da take dagewa wajen aikata laifukanta da sunan daukacin al'ummar Yahudawa.

Tambaya: Menene bambancin tsakanin sahayoniyanci a matsayin ra'ayin siyasa (ideology) da kuma addinin Yahudanci?

Amsa: Fahimtar babban bambancin da ke tsakanin Yahudanci da sahayoniyanci yana da matuƙar muhimmanci. Yahudanci addini ne, addini ne kawai. Komai a cikin Yahudanci ya ginu ne a kan imani da Allah Maɗaukakin Sarki da bin umarninsa; babu siyasa ko nuna kishin ƙasa (nationalism) a cikinsa, kuma tabbas babu laifi ko zalunci.

Yayin da sahayoniyanci ƙungiya ce ta siyasa zalla wadda mutanen da ba sa bin dokokin Yahudanci suka kafa ta, kuma suke mummunan amfani da addinin da suka ƙi bi wajen halatta laifukan da addinin kansa ya haramta.

Tambaya: Ta yaya kuke yaƙar wannan ra'ayin (sahayoniyanci) wanda, kamar yadda kuka faɗa, yake ɓata hoton Yahudanci?

Amsa: To, ƙungiyar sahayoniyanci, kamar yadda na faɗa, barazana ce ga bil'adama kuma ɓata sunan Allah ne. Hanyar da muke bi wajen yaƙar ta ita ce ta wayar da kai da ilmantarwa. Mutane suna da ƙarancin bayanan da suka dace. Kafafen yaɗa labarai na duniya ba sa isar da muhimman bayanan da mutane ke buƙata domin yanke hukunci na adalci.

Muna nan ne domin mu koyar, muna nan ne domin mu faɗaɗa wayar da kai da bayyana abin da Yahudanci ya koyar game da wannan yanayin. Ta hakan muke taimaka wa mutane su fita daga tarkon farfagandar sahayoniyanci, mu taimaka musu su fahimci abin da ke faruwa, kuma su gane cewa kasancewa mutumin kirki mai adalci ba yana nufin mutum mai ƙiyayya ga Yahudawa (antisemitic) ba ne. Bai kamata mutane su ji tsoron ɗaga muryoyinsu don yaƙar wannan zaluncin ba.

Tambaya: Shin abin da kake magana a kai, yana da kamanceceniya da abin da ke faruwa a siyasance a cikin Isra'ila game da tilasta wa Yahudawa masu tsananin addini shiga aikin soja?

Amsa: To, waɗancan matasan da ke ƙasa mai tsarki (Falasɗinu) waɗanda suka ƙi yin aikin soja a Isra'ila, ba su yi imani da gwamnatin Isra'ila ba. Suna fafutuka kuma suna yin duk abin da za su iya don kada su aikata waɗancan laifukan da hannunsu, kuma ba za su shiga cikin wannan tawaye ga Allah ba ta hanyar ba da goyon baya ga aikin sojan.

Abin takaici, waɗannan samari da 'yan mata, da zaran sun kai shekaru goma sha bakwai, ana ɗaukar su masu laifi kai tsaye kawai don sun ƙi shiga aikin soja. Ina da aboki da ya gudu daga Isra'ila domin ba ya son rayuwa a ƙarƙashin wannan tsarin, amma 'ya'yansa biyu sun kasa barin ƙasar, domin idan sun je filin jirgin sama, za a kama su.

Tambaya: Yaya kake kallon wannan artabu da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a Gaza?

Amsa: Yanayin yana da muni sosai. Mun yi imani cewa abin da ke faruwa bai fara yau ba, ko jiya, ko shekaru biyu da suka wuce, ko ma shekaru 16 da suka wuce lokacin da aka fara killace Gaza. Wannan ya fara ne tun farkon kafuwar sahayoniyanci, tun shekaru 77 da suka gabata ko ma kafin hakan lokacin da ƙungiyoyin sahayoniyanci suka fara ƙwace ƙasa kimanin shekaru 100 da suka wuce.

Kamar yadda na faɗa, wannan wani lilo ne da ba shi da ƙarshe. Abin takaici, muddin ba a magance asalin matsalar ba, wato mamaye ƙasa, to ba na ganin ƙarshen wannan rigimar.

Tambaya: Wane saƙo kake da shi ga matasan da ke cikin Isra'ila? Me kake son gaya musu?

Amsa: Abin da nake son gaya wa mutane a Isra'ila shi ne lokaci ya yi da za su farka su fahimci cewa akwai kuskure a cikin wannan tafarkin. Dole ne mu gane cewa alkawuran da sahayoniyanci ya yi mana — na tsaro, na kariya, da kuma samar da gida ga Yahudawa — alkawura ne na ƙarya, kuma tun farko sun saɓa wa rukunnan addinin Yahudanci. Abin takaici, ana ta aiwatar da laifuffuka masu yawa, akwai zalunci babba sannan hadari ne babba ga kowane bangare.

Dole ne mu janye hannunmu daga taimakawa sahayoniyanci, dole ne mu janye cewa mu daga cikin su muke. Matukar tsarin sahyoniyanci yana nan, kowa yana cikin hadari, ciki kuwa har da Yahudawa.

Ina ƙarfafa kowane Bayahude, namiji ko mace, da su bar ƙasar, domin rayuwarsu tana cikin haɗari, lafiyar hankalinsu tana cikin haɗari, kuma addininsu na Yahudanci yana cikin haɗari. Wurin nan yana da haɗari, kuma muna ƙarfafa mutane su watsar da farfagandar sahayoniyanci, su bar gwamnatin Isra'ila, su koma ga tsohon tarihinmu na zaman lafiya kafin zuwan sahayoniyanci.

Tambaya: Shin ka yarda da tsarin nan na samar da ƙasashe biyu (Two-state solution)?

Amsa: A'a. Na yarda da ɓangaren da za a mayar wa Palasdinawa ƙasarsu, amma ban yarda da barin wani ɓangare a hannun ƙungiyoyin sahayoniyanci ba, domin hakan kuskure ne a addinin Yahudanci kuma hakan ba zai kawo adalcin da muke buƙata ba.

Abin da muke faɗa shi ne dole ne a kawo ƙarshen wannan mamayar ta sahayoniyanci a Falasɗinu gaba ɗaya, a mayar wa dukkan waɗanda aka zalunta haƙƙoƙinsu, a bar dukkan 'yan gudun hijira su dawo, sannan a bar mazauna Falasɗinu na asali su zaɓi gwamnatin da suke so.

Tambaya: Yaya kake tunanin ƙasar da Yahudawa za su zauna a ciki, ƙasar Falasɗinawa ko ƙarƙashin gwamnatin Isra'ila?

Amsa: Dole ne mu duba tarihi don amsa wannan tambayar. Mun riga mun ga abin da ke faruwa a gwamnatin Yahudawa (Isra'ila); keta addinin Yahudanci ne kuma ba ya kawo zaman lafiya. Amma kasancewar ƙasar Falasɗinu ƙarƙashin ikon Musulmi, mun fuskanci hakan a baya kuma ya yi nasara sosai. Haka abin yake fiye da shekaru 100 da suka wuce, kuma wannan shine abin da ya kamata mu nema a nan gaba.

Malamanmu a ƙasa mai tsarki suna cewa suna son gwamnatin da ba ta sahayoniyanci ba, kuma ba su damu da wace irin gwamnati Falasɗinawa za su zaɓa ba, koda kuwa gwamnatin Musulunci ce mai tsananin addini, za ta fi yanayin da ake ciki yau sau dubu. Gwamnatin Musulunci za ta fi kare Yahudawa da mutunta addinin Yahudanci fiye da yadda ake yi yau.

Tambaya: A ƙarshe, menene ra'ayinka game da ƙasashen Larabawa da ke ƙoƙarin ƙulla alaƙa da Isra'ila (normalization) da kuma goyon bayan da Amurka ke ba Isra'ila?

Amsa: Ni mabiyin addinin Yahudu ne kuma zan iya ba da ra'ayin addini kan abin da ke faruwa. Abu ne mai ban takaici da tada hankali yadda muke ganin makahon goyon baya da ake ba Isra'ila, alhali kuwa hakan tawaye ne ga Allah da kuma lalata dan adamtaka. Kuma hakan yana shafar dukkan mutanen da suke da hannu a cikin wannan al'amari.

Muna fata kuma muna kira ga 'yan siyasa da su daina bin farfaganda, su sake duba alaƙarsu da Isra'ila, sannan su tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin ɗan Adam.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha