Bisa rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Hazrat Ayatullah Jawadi Amoli a yayin zaman karatun tarbiyya (Darasin Akhlaq) da ci gaba da bayani kan littafin Nahjul Balagha, ya yi fashin baki kan kalma ta 191 daga cikin gajerun maganganun sarkin muminai Ali (AS).
Ya karanta magana mai haske ta Hazrat Amir (AS) wadda ke cewa: "Lallai mutum a duniya tamkar wani abin harbi ne da mutuwa ke jifa da kiban ta a kansa..." Inda ya bayyana cewa: "Wannan magana mai haske tana fassara duniya ne yadda take, tana nuna cewa mutum a duniya kullum yana fuskantar kibau din mutuwa da hadura, ko da yake saboda shagaltuwa da wasanni, ba ya jin wannan gaskiyar."
Hazrat Ayatullah Jawadi Amoli ya ce: "Mutum domin ya amfana da lokaci da kasa, dole ne ya biya farashi mai nauyi, kuma wancan farashin ba komai ba ne face rayuwarsa (shekarunsa). Mutum domin ya yi amfani da dare da rana, da zama a doron kasa da amfana da ni'imomin dabi'a, yana bayar da rayuwarsa wadda ita ce babban jarin sa, kuma a madadin haka, yana karɓar abu mai wucewa wanda ba ya dorewa."
Malamin ya ƙara da cewa: "Babu wani jin daɗi a duniya da ba shi da wahala. Duk wani abu da ke faruwa a rayuwar mutum, akwai wani nau'i na zafi da radadi a tare da shi. Bakin ciki sune wadancan haduran da ke shake makogwaro wadanda mutum ba zai iya fitar da su daga ransa da zuciyarsa cikin sauki ba. Mutum ba ya samun wata rana ta rayuwarsa, face sai ya rasa wata ranar. Karuwar rana guda a rayuwa ba yana nufin kiyaye kwanakin baya ba ne, a'a, kullum yana tafiya ne tare da rasa wani bangare na jarin rayuwa; wannan ba riba ba ce kuma ba kudin shiga ba ne."
Ya ci gaba da bayyana cewa: "Rashin lafiya, radadi, bakin ciki, da raguwar karfin jiki da na hankali a hankali, duka wadannan makamai ne da ke taimaka wa mutuwa. Mutum a hankali yana rasa wani bangare na haddar sa, karfin sa, fasahar sa, da kuzarin sa, kuma wannan tsari shine harbin kibiya na mutuwa zuwa ga mutum a hankali kuma a jere."
Hazrat Ayatullah Jawadi Amoli yayin da yake ishara da ayar nan: "Ranar da zai tara ku don ranar taro, waccan ita ce ranar yaudara (hasara)", ya tabbatar da cewa: "Ranar Kiyama ba ranar ciniki ba ce, face ranar bayyanar hasara ce. Hasarar mutane a duniya za ta bayyana ne a ranar Kiyama, kuma a waccan ranar, za a yaye labule daga gaskiyar cinikai na yaudara da mutum ya yi a duniya.
A bangaren karshe na jawabinsa, yayin da yake ishara da kalmomin Sarkin Muminai (AS), ya bayyana cewa: "Bai kamata mutum ya shagaltu da tara dukiya fiye da bukatarsa ta hakika ba; domin abin da ya wuce bukata, a gaskiya yana mayar da mutum ne ya zama ma'ajin (mai gadin dukiya) wasu daban."
Haka nan kuma ya yi ishara da magana mai haske da ke cewa: "Lallai zukata suna da lokacin nuna sha'awa (fuskanta) da lokacin nuna gajiya (juya baya)", inda ya jaddada mahimmancin yin amfani da lokacin da zuciya take da kuzari domin koyon ilimi, inda ya ce: "Lokacin da zuciya take da sha'awa da shiri, shine mafi kyawun dama domin karantar ilimi da ma'arifa; domin ilimin da aka samu a irin wannan yanayi, zai yi tasiri a ran mutum kuma zai dore."
Your Comment