A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, ƙasar jamhuriyyar Musulunci ta Iran a ranar murnar haihuwar Sayyida Fatima Zahra (AS), ta kasance cikin haske, farin ciki da murna. Saboda wannan, an gudanar da wani babban taro a Hussainiyyar Imam Khomeini (RA) wanda Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da dubban masu son Gidan Annabi (AS) suka halarta, inda aka gudanar da shagulgulan bege, wakoki da yabon Uwargidan Matan Duniya.
A wannan taron wanda ya kusan tsawon sa'o'i uku, Mai Girma Ayatullah Khamene'i, tare da taya murna da haihuwar Sayyida Fatima (AS), ya ce: "Al'ummar Iran ta hanyar juriya, sun hana kokarin da maƙiyan ke yi na canza 'asalin addini, tarihi da al'adun' wannan al'umma, kuma a yau, tare da bukatar shirya daidaitaccen tsarin kariya da kai hari a gaban ayyukan tallace-tallacen makiya da na kafofin watsa labaran maƙiya don kai hari ga 'tunani, zukata da imani,' Iran mai girma tana ci gaba da tafiya ta gaba duk da matsaloli da karancin abubuwan da ake da su a ko'ina cikin ƙasa."
Jagoran Juyin Juya Halin, ya girmama haɗuwan ranar haihuwar Imam Khomeini (RA) da ta Mai girma Fatima (AS), ya ɗauki halaye da darajojin uwargidan duniyoyin biyu (duniya da lahira) sama da fahimtar ɗan adam, ya kara da cewa: "Duk da haka, dole ne a kasance kamar Fatima, kuma a bi wannan uwargida a kowane fanni ciki har da ibada, neman adalci, jihadin bayyana gaskiya, zamantakewa da miji, tarbiyyar yara da sauran fannoni."
Ya kuma bayyana mawaka a matsayin masu tasiri sosai, ya kara da cewa: "Ya zama dole a yi bincike da nazari don zurfafa fahimta, bincika illoli da nemo hanyoyin ƙarfafa da haɓaka sassa daban-daban na wannan al'amari mai ban mamaki."
Mai Girma Ayatullah Khamene'i, yana nuni ga ci gaban yabon idan aka kwatanta da baya, ya nuna yabon a matsayin ɗaya daga ci gaban adabin muƙawama, ya kara da cewa: "Duk wani tunani ko al'amari idan bai sami adabin da ya dace ba, sannu a hankali zai ɓace, kuma waka da hai'o'i, a yau, ta hanyar tsarawa, faɗaɗawa da isar da adabin gwagwarmaya, suna ƙarfafa wannan muhimmiyar bukata ta musamman."
Jagoran Juyin Juya Halin ya ayyana 'juriyar ƙasa' a matsayin 'jurewa da tsayawa tsayin daka a gaban kowane irin matsin lamba na masu mulkin mallaka,' ya kara da cewa: "Wani lokaci matsin lamba na soja ne; -kamar yadda al'umma suka gani a lokacin yaƙin da aka yi watannin da suka gabata kuma samari da matasa suka kuma gani- wani lokacin kuma matsin lamba na tattalin arziki ne ko na kafofin watsa labarai da na al'adu da na siyasa."
Jagoran Juyin Juya Halin ya kira tashe-tashen hankula da tada hankali da kafofin watsa labarai da jami'an siyasa-soja na Yammacin duniya ke yi a matsayin wani nau'i na matsin lamba na tallace-tallacen maƙiya, ya kuma ce: "Manufar matsi iri-iri na tsarin mulkin mallaka a kan al'ummomi, kuma a kan gaba da su al'ummar Iran, wani lokaci neman faɗaɗa ƙasa ne; kamar abin da gwamnatin Amurka ke yi a yau a Latin Amurka."
Ya kara da cewa: "Wani lokacin kuma samun iko da albarkatun ƙarƙashin ƙasa shine manufa, wasu lokuta kuma canza salon rayuwa, kuma mafi muhimmanci, 'canza asali,' shine babban burin masu mulkin mallaka."
Mai Girma Ayatullah Khamene'i, da yake nuni ga shekaru sama da ɗari na kokarin azzaluman duniya don canza asalin 'addini, tarihi da al'adu' na al'ummar Iran, ya ce: "Juyin Juya Halin Musulunci ya sa duk wadannan ayyukan suka zama na banza da wofi, kuma a cikin 'yan shekarun nan, al'umma ta hanyar rashin sallamawa da tsayawa tsayin daka a gaban ci gaban matsin lamba da maƙiyanta suke yi, sun hana su."
Ya kira faɗaɗa ma'ana da adabin muƙawama daga Iran zuwa ƙasashen yankin da wasu ƙasashe daban a matsayin gaskiya, ya kara da cewa: "Wasu ayyukan da maƙiyan ke yi wa Iran da al'ummar Iran, da wasu ƙasashen ake yi wa, da wannan al'umma da ƙasar za ta zama sai yadda suka yi da ita."
Jagoran Juyin Juya Halin, lokacin da yake nuni ga tasirin wakokin Zainabiyya a cikin dawwamar da tunawa da shahidai da zurfafa ma'anar juriya a cikin ƙasar, ya ce: "A yau, fiye da rikice-rikicen soja da muka gani, muna cikin 'tsakiyar yaƙin tallace-tallace da kafofin watsa labarai' na maƙiya; domin maƙiyan sun fahimci cewa wannan ƙasar ta Allah, ba za a iya sallama ko kwace ta da matsin lamba na soja ba."
Ya kara da cewa: "Tabbas wasu suna yawan ambaton yiwuwar sake yin yaki na soja, wasu kuma da gangan suna hura wannan batu don su sa mutane su kasance cikin shakku kuma su haifar da firgici, amma da yardar Allah ba za su yi nasara ba."
Mai Girma Ayatullah Khamene'i ya ɗauki "manufa, haɗari da burin maƙiyan" a matsayin shafe "sakamakon, manufofi da ma'anoni na juyin juya hali da mantawa da tunawa da Imam Khomeini (RA)," ya kara da cewa: "Amurka tana kan gaba a wannan aiki, da kuma wasu ƙasashen Turai a tare da su, sai kuma wasu maha'inta marasa kishin ƙasa waɗanda ke Turai suna fafutikar samun abin ci."
Ya ɗauki sanin manufofi da "tsarin maƙiyan" a matsayin larura, ya ce: "Kamar bangaren soja, a cikin wannan rikicin, a bangaren tallace-tallace da kafofin watsa labarai ma dole ne mu ayyana tsarinmu daidai da shiri da tsari da burin maƙiyan, kuma mu mai da hankali kan wuraren da suke kai hari, wato 'ilimin addinin Musulunci, Shi'a da na juyin juya hali'."
Babban Jagoran Juyin Juya Halin ya bayyana tsayawa tsayin daka a gaban yaƙin tallace-tallace da kafofin watsa labarai na Yammacin duniya a matsayin wanda ke da wahala amma yana yiwuwa sosai, ya kuma ce: "A kan wannan hanya, mawaka da masu yabo su mayar da wuraren majalisinsu cibiyoyin riƙo da kimar juyin juya hali, kuma tare da godiya ga sha'awar matasa ga yabon da kuma tarukan addini, mawakan su kare wadannan matasa daga burin maƙiyan da suke da kayan aiki, masu taurin kai da mugun nufi."
Babban Jagoran Juyin Juya Halin ya kammala jawabinsa tare da wasu shawarwari ga masu yabon: Bayyana ilimin addini da ilimin gwagwarmaya bisa rayuwar dukkanin Shugabannin shiriya (AS), kai hari ga raunin maƙiyan tare da bada kariya mai inganci a gaban shakkun da yake haifarwa, bayyana ma'anoni na Alƙur'ani a fannoni daban-daban na 'yan adamtaka, zamantakewa, siyasa da yadda ake fuskantar maƙiyan' na daga cikin muhimman shawarwarin.
Ya kira tasirin waka mai kyau da ma'ana da cewa wani lokacin ya fi tasirin wasu litattafai da jawabai, ya kuma ce: "Mawakan su kula kada waƙoƙi da al'adun zamanin mulkin dawagitai su shiga cikin majalisinsu da tarurrukansu."
A ƙarshen jawabinsa, Mai Girma Ayatullah Khamene'i, yana nuni ga jawabin wani mawaki game da matsalar ƙurar Khuzestan, ya ce: "Wannan, yana ɗaya daga cikin ƙananan matsaloli, kuma karancin abubuwa da matsaloli suna da yawa a duk faɗin ƙasar amma kowace al'umma tare da tsayawa tsayin daka, gaskiya da tsaftar zuciya da neman alheri da neman adalci, tana haifar da kima da mutunci da ƙarfi ga Musulunci da Iran, kuma da taimakon Allah, ƙasar tana tafiya, ƙoƙari da ci gaba."
A farkon wannan ganawa goma sha ɗaya daga cikin masu yabon Gidan Annabi (AS) sun yi wakoki da kuma yabo.
21:06 - 2025/12/13
Your Comment