Saturday 6 December 2025 - 13:35
Shawarwarin Musulunci Sune Mahadin Ilmi da Addini

Hauza/ Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun ilmin addinin Musulunci (Hauza) ya bayyana cewa addini shi ke kawo haɓakar ilmi. Ya ce: "a kan wannan tushen, yayin shawarwari, tare da girmama ilmi, ya kamata mu yi ƙoƙari cewa nasarorinmu su kai ga samar da sababbin ababen koyi".

A rahoton ofishin yada labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun ilmin addinin Musulunci (Hauza) yayin wani taro na hadin gwiwa tsakanin shugaban hukumar kula da lafiya ta ƙasa tare da shugabannin cibiyoyin shawarwari na Samah a duk faɗin ƙasar da aka yi a zauren taro na makarantar ilmin addini ta Ma'asumiyya a birnin Qum, Ayatullah A'arafi ya bayyana cewa: "Ayyukan cibiyoyin shawarwari na Samah na makarantun ilmin addini, a cikin makarantun Hauza abin yabawa ne domin ku bangaren kiwon lafiya ne a cikin makarantun, haka kuma babban aikin da kuke yi na hidimtawa jama'ar ƙasa da kuma hidimar da kuke bayarwa abin yabawa ne."

Shugaban makarantun ilmin addini ya ci gaba da cewa: "Lokacin da muke magana kan shawarwari na Musulunci ko ilimin halayyar dan adam ta fuskar Musulunci, muna tsakiyar ra'ayoyi biyu da ba su dace ba, muna bayyana ra'ayi na uku a cikin kafa ilimin ɗan adam da ilimin shawarwari, kuma mun yi imani da shi."

Ayatullah A'arafi ya bayyana: "Ra'ayi na ɗaya shi ne a dogara ga shawarwari da siffar da ta samo asali daga yammacin duniya. Ilimin halayyar ɗan adam da ake gani a cikin ilimin ɗan adam na yammacin duniya, wanda ba a ba da ƙima ga ainihin abin da ke cikin ɗan adam ba."

Ya kara da cewa: "Ra'ayi na biyu shi ne a dogara ga tushen addinin Musulunci kawai wanda abin da ake nufi shi ne cewa ba ma buƙatar ilimi da gogewa, a haƙiƙa ya zama muna da ra'ayoyi marasa zurfi, wanda shi ma ra'ayi ne da ba za mu yarda da shi ba."

Shugaban makarantun ilmin addini na ƙasar ya jaddada cewa: "Ra'ayi na uku kuma na gaskiya shi ne mu kafa dangantaka tsakanin ilimin Musulunci da misalan addini tare da gogewar ɗan adam, ta yadda za su zama masu kammala juna."

Ya ci gaba da cewa: "A fagen shawarwari ma, mun yi imanin cewa ya kamata mu yi amfani da gogewar ɗan adam, kuma addinin kansa ya kira mu zuwa ga hakan, wanda a cikin Alkur'ani an kawo karamomin ɗan adam."

Ayatullah A'arafi, tare da bayyana cewa addini yana haɓaka ilimi, ya bayyana cewa: "A kan wannan tushe, a yayin shawarwari, yayin da muke girmama ilimi, ya kamata mu yi ƙoƙari cewa abin da muka samu ya kai ga samar da sababbin ababen koyi."

Ya kara da cewa: "Falsafar shawarwari ta fuskar Musulunci ko bincike na asali a fagen ilimin ɗan adam, ɗaya ne daga cikin ayyukan da cibiyoyin shawarwari na Samah na makarantun ilmin addini suka kamata su yi."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha