Rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayyana cewa, a mahangar Shi'a, Imami kuma magajin Annabi ana zaɓar sa ne kawai ta hanyar umarnin Allah da zaɓinSa, sannan Annabi ya sanar da mutane shi. Saboda haka, babu wani mutum ko wata kungiya da ke da ikon tsoma baki a cikin wannan lamarin.
Akwai dalilai da dama da suka nuna wajibcin nada Imami daga wurin Allah, daga ciki akwai:
A. Kamar yadda Alƙur'ani ya bayyana, Allah ne kawai mai iko a kan komai. Wannan ikon na Allah ne Shi kadai, kuma Shi ne zai mika shi ga wanda ya cancanta. Kamar yadda aka zaɓi Annabi ta hanyar wahayi, Imami ma Allah ne ke nada shi domin ya kasance waliyyi a kan mutane.
B. Mun riga mun yi bayanin cewa Imami dole ya kasance Ma'asumi (wanda ba ya kuskure) kuma masanin komai. A bayyane yake cewa, gano mutumin da yake da waɗannan siffofin a matsayi mafi girma, ba zai yiwu ba sai ta wurin Allah Maɗaukakin Sarki, wanda Shi kadai ne masanin abin da ke bayyane da abin da ke ɓoye a cikin zukatan mutane.
Kamar yadda Allah ya faɗa wa Annabi Ibrahim (A.S):
"Lallai Ni zan sanya ka ka zama Imami ga mutane." (Baqarah: 124).
Game da Annabi Adam (A.S) kuma ya ce:
"Lallai fa Ni zan sanya Halifa (wakili) a bayan ƙasa." (Baqarah: 30).
Haka ma ya faɗa wa Annabi Dawuda (A.S):
"Ya Dawuda! Lallai Mu Mun sanya ka ka zama Halifa a bayan ƙasa, saboda haka ka yi hukunci a tsakanin mutane da gaskiya." (Sad: 26).
Haka ma ya faɗa wa Annabi Muhammad (S):
"Ya kai Annabi! Lallai Mu Mun aike ka ka zama shaida, kuma mai bishara, kuma mai gargaɗi." (Ahzab: 45).
Sannan kuma ya ce:
"Kuma Mun sanya daga cikinsu Imamai (shugabanni) waɗanda suke shiriyarwa da umarninMu sa’ad da suka yi haƙuri, kuma sun kasance suna da yaƙini da ayoyinMu." (Sajdah: 24).
Saboda haka, nada shugaba da Imami hakkin Allah ne Shi kadai.
Kyawawan Kalamai Daga Imam Rida (A.S) Game da Matsayin Imami:
Imam Rida (A.S) ya bayyana girman matsayin Imami da cewa:
“...Shin mutane sun san girman matsayin Imami da kuma matsayinsa a cikin al’umma, har ya kasance zaɓin hakan ya zama a hannunsu? Lallai Imami ya fi girma, ya fi daukaka, matsayinsa ya fi kowane wuri sarari, kuma zurfinsa ya fi yadda mutane za su iya kaiwa gare shi da hankalinsu, ko su same shi da ra’ayoyinsu, ko su nada Imami da zaɓin kansu."
Ya ci gaba da cewa:
“Lallai Imami shi ne tushen Musulunci mai girma, kuma reshensa mai ɗaukaka. Ta hanyar Imami ne ake cika Sallah, Zakkah, Azumi, Hajji, da Jihadi. Da shi ne ake samun yalwar dukiya da sadaka, da aiwatar da hukuncin Allah, da tsaron iyakokin ƙasa. Imami shi ne yake halatta abin da Allah ya halatta, kuma yake haramta abin da Allah ya haramta, ya tsayar da dokokin Allah, ya kare addinin Allah, kuma ya kira mutane zuwa ga hanyar Ubangijinsa da hikima, da wa’azi mai kyau, da hujjoji bayyanannu."
"Imami shi ne guda ɗaya tilo a zamaninsa; babu wanda ya kai kusa da shi, babu wani malami da ya yi daidai da shi, ba a samun madadin sa, kuma ba shi da kamanceceniya ko misali, An keɓance shi da dukkan falala ba tare da ya neme ta ba ko ya yi ƙoƙarin neman ta ba, face dai wata baiwa ce da Allah Mai bayarwa Ya keɓance shi da ita saboda falalarSa. To, wane ne zai iya kaiwa ga sanin haƙiƙanin Imami, ko kuma ta yaya zaɓar sa zai yiwu ga mutane?..." (Usulul Kafi, juzu'i na 1, shafi na 198).
Wannan bayani zai ci gaba...
An ciro ne daga littafin “Negin-e Afarinesh”, tare da ɗan sauyi kadan.
Your Comment