Bisa rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, jerin tattaunawa kan Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ilimin da ya shafi Imam Mahdi (A.S), yake gabatar muku da wannan maudu'i.
Ɗaya daga cikin siffofi mafi muhimmanci na Imami kuma sharadi na asali na Imamanci shi ne "Ismah".
"Ismah" wata siffa ce ta dabi'a (malakah) da take fitowa daga cikakken ilimi game da gaskiyar al'amura da kuma ƙaƙƙarfan nufi. Sakamakon mallakar waɗannan abubuwa guda biyu, Imami yana kiyaye kansa daga aikata kowane irin zunubi ko kuskure.
Imami ma'asumi ne (wanda aka kiyaye) daga kowane irin tuntuɓe ko kuskure, walau a wajen fahimta da bayyana koyarwar addini, ko a wajen aikata su, ko kuma a wajen gano maslahar al'ummar Musulmi.
Akwai dalilai na hankali da na nassi (daga Alkur'ani da Hadisai) game da Ismar Imami. Ga manyan dalilan hankali:
A. Tsare Addini: Kare addini da hanyar bauta ya dogara ne ga Ismah na Imami; domin Imami ne ke da alhakin kare addini daga karkatarwa da kuma jagorancin mutane. Ba maganarsa kaɗai ba, har ma da ayyukansa da amincewarsa ko rashin amincewarsa ga ayyukan wasu, suna yin tasiri ga dabi'un al'umma. Saboda haka, dole ne ya kasance amintacce daga kowane tuntuɓe a fahimtar addini da aikata shi, domin ya jagoranci mabiya zuwa ga hanya madaidaiciya.
B. Dogara da Amincewa: Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa al'umma ke buƙatar Imami shi ne cewa mutane ba su da kariya daga kuskure wajen sanin addini da aiwatar da shi. To, idan shi ma shugaban mutanen yana kuskure, ta yaya za su ba shi cikakkiyar amana?! Ma'ana, idan Imami ba ma'asumi ba ne, mutane za su kasance cikin shakka wajen bin umarninsa.
Bugu da ƙari, idan Imami yana yin kuskure, to za a buƙaci wani imamin daban don ya gyara masa, idan shi ma wannan na biyun yana kuskure, to za a buƙaci wani... wannan jerin ba zai taɓa ƙarewa ba, wanda hakan a wajen ma'abota hankali barna ne (Logical Fallacy).
Dalilin Alkur'ani:
Akwai ayoyi da dama da ke nuna wajibcin Ismah, ɗaya daga cikinsu ita ce aya ta 124 a cikin Suratul Baqarah. A cikin wannan aya, Allah Madaukakin Sarki ya ba Annabi Ibrahim (A.S) matsayin Imamanci bayan matsayin Annabta. A lokacin ne Annabi Ibrahim (A.S) ya roƙi Allah ya sanya Imamanci a cikin zuri'arsa.
Allah Madaukakin Sarki ya amsa masa da cewa: "Lā yanālu ‘ahdī al-ẓālimīn" (Alkawari na - wato Imamanci - ba zai taɓa samun azzalumai ba).
Wannan yana nuna cewa:
1. Duk wanda ya taɓa yin shirka ko zunubi, to ya zalunci kansa ko ya yi zalunci ga Allah.
2. Alƙur'ani ya kira zunubi da sunan "Zalunci".
Don haka, duk wanda ya taɓa yin zunubi a rayuwarsa, to ya faɗa cikin rukunin "Azzalumai", saboda haka bai cancanci matsayin Imamanci ba.
Sakamakon wannan bayani shi ne: Matsayin Imamanci daga Allah yana tabbatuwa ne kawai ga waɗanda ba su taɓa aikata zunubi ko kuskure ba a duk tsawon rayuwarsu.
Wannan bayani zai ci gaba...
(An naƙalto daga littafin "Negin-e Afarinesh")
Your Comment