A wani rahoto daga sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, Majalisar Malaman Shi'a ta Indiya, ta hanyar fitar da wata sanarwa a hukumance, ta yi Allah wadai da mafi tsananin kalmomi game da barazanar da Donald Trump ya yi kwanan nan ga Hazrat Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Husaini Khamenei (Allah ya kara masa albarka) Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, inda ta kira shi "Bugun Zukatan Marasa Galihu na Duniya kuma Fatan Mazalumai na Falasɗinu."
Rubutun wannan Sanarwar Shine Kamar Haka:
DA SUNAN ALLAH, MAI RAHMA, MAI JINƘAI.
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin Talikai, kuma tsira da Aminci su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad da kuma iyalansa tsarkaka.
A yau duniya, musamman al'ummar Musulmi, tana fuskantar daya daga cikin matsanancin lokuta masu muhimmanci da kuma kafa tarihi. Shugabannin tinƙahon duniya suna watsi da ka'idojin ilimi, na bil'adama, da kuma dokokin kasa da kasa, tare da dogaro da karfi da girman kai, musamman Amurka da abokiyar zamanta ta Sahyoniyyanci, Isra'ila, sun sanya tsaron duniya da kwanciyar hankali cikin hadari.
Barazana da makirci kan babban, Babban Marja'in duniyar Musulunci, masanin Fikihu kuma Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, ba wai kawai ya shafi wani mutum ba ne; a'a, yana nufin cin zarafi a fili ga darajar al'ummar Musulmi da kuma asalin ta. Wannan aiki ba kawai banbancin siyasa ba ne, amma wata sanarwa ce ta ƙiyayya ga Musulunci da kuma Musulmi.
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ba wai shugaban siyasa kawai na wata kasa ba ne, wani marja'in addini ne mai daraja ga Musulmi da kuma masu 'yanci a duk fadin duniya. Muryar 'yantar da Birnin Qudus mai alfarma, fatan azzalumai na Falasɗinu, kuma tushen kwarin gwiwa ga al'ummar masu juriya (muƙawama) a Lebanon, Yemen, da Iraƙi, sun hade da hikimarsa da jagorancinsa. Sirarsa da kuma basirarsa suna koya mana cewa a gaban zalunci, hanyar muminai ba ta kasance mika wuya ba, sai dai ta tsayawa da ilimi, tare da hakuri, hikima, da hadin kai.
An ci gaba da cewa: Majalisar Malamai 'Yan Shi'a ta Indiya, tare da cikakken ɗaukar nauyin mas'uliyya ta bayyana cewa duk wata barazana ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a zahirin gaskiya, kamar kalubalantar dukkan al'ummar Musulmi ce, kuma irin wannan hanya ta sabawa ka'idojin dan adamtaka, ka'idojin kasa da kasa, da kuma koyarwar Musulunci ne.
Wannan sanarwar ta kare da kira ga kowa da kowa: An yi kira ga dukkan malaman addini, masu tunani, jiga-jigan siyasa da zamantakewa, da kuma dukkan mutanen da ke masu 'yanci da kuma masu hankali, su kawar da dukkan banbancin aƙida da ra'ayi su yi Allah wadai da wannan zaluncin kuma su tsaya a kan gaskiya da adalci. Daga karshe muna rokon Allah ƙarin lafiya, daukaka da nasara ga jagoran juyin juya halin Musulunci, haka kuma muna addu'ar Allah ya kara hada kan al'ummar musulmi tare da bawa mazalumai nasara cikin gaggawa.
Hujjatul Islam Jawad Haidar Razawi, Majalisar Malaman Shi'a ta Indiya
Your Comment