A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, a ranar farko ta mako mai albarka na Ranakun Nasara Fajr (Dahe Fajr), jagoran juyin juya halin Musulunci a ganawa da dubban mutane daga sassa daban-daban na al'umma, ya kira ranar 12 ga watan Bahman keɓantacciyar rana kuma mai tarihi. Da yake yin ishara da canza mulkin "na mutum ɗaya, na zalunci, na adawa da addini da rashin yanci" na Shah Pahlavi zuwa gwamnatin " jama'a, bisa addini da tsayawa a gaban zalunci", ya ce: "Jama'a sun kashe wutar tarzomar Amurka da Isra'ila na kwanan nan kamar yadda suka yi wa duk wani makirci da suka gabata, kuma a nan gaba ma, al'umma za su cimma burinsu a kan kowane bala'i da taimakon Allah."
Hazrat Ayatullah Khamenei har ila yau, ya bayyana ƙoƙarin Amurka na haɗiye Iran da tsayin daka mai ƙarfi na al'umma a gaban wannan sha'awar a matsayin ainihin dalilin adawa na shekaru 47 tsakanin Iran da Amurka. Da yake yin ishara da kalaman Amurkawa na baya-bayan nan, ya kara da cewa: "A baya ma, don tsoratar da al'ummar Iran, sukan ce 'duk zaɓuɓɓukan suna kan tebur.' Kuma lalle ne su sani cewa idan wannan karon suka kaddamar da yaki, 'zai zama yakin yanki.'"
A farkon jawabinsa, da yake yin ishara da tarbar gaba ɗaya kuma mara misali na al'umma ga Imam Khomeini (RA) a ranar 12 ga Bahman, shekara ta 1357 (01 ga Fabrairu, 1971), ya ce: "Imam a cikin duk barazanar da ake yi masa, da ƙarfin hali da ƙarfi ya shiga birnin Tehran, kuma ya mai da babbar tarbar ban mamaki ta jama'a a matsayin wani abu na kafa sabuwar gwamnati, kuma a wannan rana ya ayyana rushewar daular sarauta."
Jagoran juyin juya hali ya bayyana canza mulkin mutum ɗaya da na zalunci zuwa mulkin da jama'a suke yin komai a cikinsa, da kuma canza tsarin adawa da addini na Pahlavi zuwa tsarin Musulunci a matsayin siffofin tsarin da ya samo asali daga jihadin Imam da al'umma. Ya kara da cewa: "Da duk masu mas'uliyya sun yi aikin da ya rataya a wuyansu, da mulkin ya zama na addini sosai, amma duk da a jumlance mun ci gaba a kan tsarin addini da na Musulunci."
Hazrat Ayatollah Khamenei ya ɗauki mayar da ƙasar ga masu ita -wato al'umma- da yanke hannu da tasirin Amurka daga Iran a matsayin wata siffa ta tsarin gwamnatin Musulunci, ya ce: "Wannan siffar ta ɓata wa Amurka rai da firgitata, kuma tun daga wannan rana ta jawo ta cikin gaba da al'umma da tsarin."
Da yake bayyana siffofin gwamnatin jama'a, ya yi ishara da haɓaka yanayin dogaro da kai a cikin al'umma inda ya ce: "Imam mai hikima, ya sanar da al'umma manyan iyawarsu da ƙimarsu, kuma ya mayar da tunanin 'ba za mu iya ba' zuwa mahimmin imani na 'za mu iya.'"
Jagoran juyin juya hali ya kira sakamakon manufofin rashin mutunci da rashin yanci na Qajar da Pahlavi ya mayar da al'umma "babba kuma mai tarihin wayewa da al'adu mai haske" zuwa mutane "masu wulakanci da koma baya." Ya ce: "A wancan zamani, a 'ilimi da fasaha, siyasa, salon rayuwa, darajar ƙasa da ƙasa, ma'auni na yanki' da kuma a kowane fanni, mun koma baya. Amma Imam Khomeini, ya busa ruhin 'dogaro da kai' a cikin al'umma, kuma ya canza hanyar zuwa digiri 180."
Jagoran juyin juya hali ya ɗauki ranar 22 ga Bahman, ranar nasarar juyin juya hali da kuma ranar 12 ga Farvardin, ranar kafa Jamhuriyar Musulunci da kuri'un al'umma da duk ci gaban ƙasar a matsayin sakamakon ranar 12 ga Bahman, shekara ta 1357 inda ya kara da cewa: "Albarkar wannan babban rana na ci gaba da falalar Allah."
A wani bangare na jawabinsa, da yake jaddada hannun Amurka da Isra'ila a "Fitinar 18 da 19 ga Dey", ya bayyana masu hargitsin a matsayin matattakalar da "shuwagabannin" da "masu tafiyar da tsarin" suka yi amfani da ita, inda ya kara da cewa: "Shuwagabannin, da yawa daga cikinsu an kama su, kamar yadda suka furta, an ba su kuɗi don ayyukansu, kuma an horar da su kan yadda za a kai hari ga cibiyoyi da tara da kuma motsa matasa; amma wani ɓangare na masu hargitsi, matasa ne masu kuzari waɗanda ba mu da matsala da yawa tare da su."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira kalaman Shugaban Amurka a matsayin bayyananniyar alama ta hannun Amurka da Isra'ila a hargitsin kwanan nan inda ya ce: "A fili yana gaya wa masu hargitsi waɗanda suke kira al'ummar Iran cewa 'Ku ci gaba, ni ma ina zuwa!' Lalle ne, bisa ga ra'ayinsu, waɗannan dubban masu hargitsi, al'ummar Iran ce, amma miliyoyin mutanen da suka yi gangami a ranar 22 ga Dey (Di) a faɗin ƙasar ba al'ummar Iran ba ne."
Hazrat Ayatollah Khamenei ya bayyana sabon tunani da hanyar Jamhuriyar Musulunci da kuma rikice-rikicen da ke tsakaninta da muradun manyan ƙasashen duniya a matsayin abin da ke ci gaba da jawo musu gaba. Sun ce: "Saboda haka, hargitsin kwanan nan, kamar yadda ba shi ne na farko a Tehran ba, ba zai zama na ƙarshe ba, kuma yana iya maimaituwa a nan gaba."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: "Wannan ƙiyayya za ta ci gaba har sai al'ummar Iran da kafaffen ra'ayi da juriya da cikakken ikon kan al'amura, sun sa abokan gaba su yanke ƙauna, wannan ma za mu kai ga shi."
Da yake yin ishara da al'amura da laifuka makamantan hargitsin kwanan nan a Tehran kamar na 30 Khordad, shekara ta 1360 (10 ga June, 1981), lokacin da munafukai suka kai wa 'yan Basij hari da manyan wukake, ya lurar cewa: "A cikin duk waɗannan al'amuran, ana iya ganin sa hannun ƙasashen waje musamman hannun Amurka da gwamnatin Isra'ila."
Jagoran juyin juya hali, da yake jaddada cewa a cikin hargitsin kwanan nan da al'amuran shekarun baya, hukumomin 'yan sanda, 'yan Basij, gungun Sojojin kare juyin juya halin Musulunci (SEPAH) da sauran sassan sun cika aikinsu sosai, ya kara da cewa: "Amma abin da ya kashe wutar tarzomar ta kuma zubar da tokarta kamar a shekara ta 88 (2009), shi ne shiga jama'a filin wasan, kuma bayan haka ma idan wani bala'i ya faru ga ƙasar, Allah Mai girma zai aiko wa wannan al'umma dan aike don yaki da ita, kuma jama'a za su kai ƙarshen aikin."
Hazrat Ayatollah Khamenei a yayin bayyana siffofin fitinar Amurka ta baya-bayan nan, ya ɗauki siffar farko a matsayin labewar masu hargitsi a bayan zanga-zangar 'yan kasuwa inda ya ce: "Masu tada hargitsi kamar masu laifi waɗanda a yayin kai hari ga garuruwa, sukan yi amfani da mata da yara a matsayin garkuwa, sun ɓoye a bayan 'yan kasuwa waɗanda suke da magana mai ma'ana da gaskiya da suka fito titi, don kada a gane su."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: "Koda yake, 'yan kasuwa masu wayo da ganin ayyukan masu hargitsi kamar kai hari ga ofisoshin 'yan sanda maimakon tafiya a hankali a titi, suka rabu da su, kuma suka bar masu tada hargitsin su kaɗai."
Ya bayyana siffa ta biyu na tarzomar kwanan nan a matsayin kamar juyin mulki, inda ya ce: "Wannan tarzomar, kamar yadda wasu a duniya ma suka yi ishara da shi, yayi kama da juyin mulki. Tabbas an magance shi, amma lalata cibiyoyi masu muhimmanci da tasiri a cikin gudanar da ƙasar ta hanyar kai hari ga 'yan sanda, cibiyoyin gungun Sojojin kare juyin juya halin Musulunci, wasu cibiyoyin gwamnati da bankuna da kuma kai hari ga abubuwan ruhaniya kamar masallatai da Alkur'ani, yana nuna wannan gaskiya."
Hazrat Ayatollah Khamenei, da yake tunawa da ci gaban ƙasar a fannoni daban-daban, ya kara da cewa: "Wane ne zai gaskata cewa al'ummar Iran za ta kai ga yau da Amurkawa su yi kwafin makamin da ta ƙera? Wadannan duka sakamakon dogaro da kai, bege da buri ne wanda Imam Khomeini a matsayin 'abin alama na bege da dogaro da kai' ya haifar a cikin al'umma, kuma ya sa jama'a sun yi ƙoƙari da kuma motsi."
Da yake tunawa da waswasi na shaidanu na zahiri na ƙasashen waje da na cikin gida kan cewa "matashin ɗan Iran, ba shi da fata da gaba," ya ce: "Matashin ɗan Iran yana da fata da kuma himma, kuma zai gina gaba ma -a makantar idanunku."
Hazrat Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa an tsara tarzomar ne a ƙasashen waje da kuma jagorantar shuwagabanninta cikin gida ta amfani da abubuwa daban-daban kamar bayanan tauraron dan adam a matsayin wata siffa ta tarzomar watan Dey (Di), ya ankarar cewa: "Dangane da bayanan da aka kawo, wani jigon Amurka mai tasiri a gwamnati, ya gaya wa abokin sa na Iran cewa hukumamin leƙen asirin CIA da Mossad sun kawo duk ƙarfin su da suke da su a wannan lamarin."
Ya bayyana aikin shuwagabannin da aka horar da su don kashe mutane a matsayin wata siffar ta tarzomar, inda ya ce: "Bisa wannan tsari, sun kai hari ga cibiyoyin soja da na 'yan sanda da manyan makamai na musamman domin a mayar da martani, mutane su mutu; koda yake don ƙarin kashe mutane, ba su ji tausayin yaransu da suka kawo ta hanyar talla ba, har ma sun kai hari ga su."
Jagoran juyin juya hali, da yake nuna bakin cikinsa kan nasarar shuwagabannin tarzoma wajen ƙara yawan waɗanda suka mutu, ya ce: "Zuciyar mutum tana yin kuna ga waɗannan matasa marasa hankali da rashin kulawa."
Hazrat Ayatollah Khamenei, da yake yin ishara da ƙoƙarin abokan gaba don nuna yawan waɗanda suka mutu sau goma, sun ce: "Suna son yawan waɗanda suka mutu ya wuce wannan; lalle ne wannan adadin hasara ma yana da matuƙar bakin ciki."
Sun kira ainihin manufar abokan gaba a matsayin rushe tsaron ƙasar, ya kara da cewa: "Duk lokacin da ba tsaro, babu komai. Ba burodi, ba ƙirƙira, ba kasuwanci, ba darasi da tattaunawa da bincike, ba ilimi da ci gaba; saboda haka waɗanda suka kiyaye tsaron ƙasar suna da haƙƙin rayuwa a wuyan dukan jama'a."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: "Sun so sanya jama'a su yi fito na fito da tsarin, amma jama'a da fitowar su na miliyoyi a ranar 22 ga Dey (12 ga Janairu) sun daki bakin maƙiyan, kuma sun nuna gaskiyar al'ummar Iran."
Da yake jaddada cewa masu mas'uliyya da gaske ya kamata su daraja waɗannan jama'a, ya ce: "Tabbas wannan tarzoma an yi ta ne bisa kuskure ko a ƙididdige a lokacin da gwamnati da masu mas'uliyya ke tsara fakitin da taswirar tattalin arzikin ƙasar don inganta yanayi."
Siffar ƙarshe da jagoran juyin juya hali ya yi ishara da ita na tarzomar kwanan nan, shi ne ta'addanci irin na Da'ish.
Da yake yin ishara da ikirari na shugaban Amurka na yanzu a zaɓen farko na wa'adin mulkinsa game da shigar da gwamnatin Amurka wajen ƙirƙirar Da'ish, ya ce: "A cikin tarzomar kwanan nan ma, 'yan Amurka sun ƙirƙiri Da'ish wanda aikinsu yayi kama da wannan Da'ish din. Da'ish ta kashe mutane da tashin hankali da zargin rashin addini, kuma waɗannan ma suna halaka mutane da wannan tashin hankalin amma saboda bin addini, kuma da mugunyar rashin tausayi mai ban mamaki, sun ƙone wasu mutane da rai, suka yanke kawuna."
Hazrat Ayatollah Khamenei a cikin bangaren ƙarshe na jawabinsa game da dalilin ƙiyayyar shekaru arba'in da suka wuce tsakanin Amurka da Iran, ya ce: "Al'amarin ya taƙaita cikin kalmomi biyu: Amurka tana son ta haɗiye Iran amma al'ummar Iran da Jamhuriyar Musulunci, suna hanawa; kuma a zahiri laifin al'ummar Iran shi ne cewa ta ce wa Amurka kuna yin kuskure don kuna son haɗiye ƙasata."
Sun ɗauki abubuwan jan hankali iri-iri na Iran kamar mai, iskar gas, arzikin ma'adanai da matsayi na dabara da yanayin ƙasa a matsayin abin da ke haifar da sha'awar ƙarfi mai kai hari da sha'awa kamar Amurka. Sun lurar cewa: "Suna neman mamaye Iran da kuma dawo da ikonsu kan albarkatu, man fetur, siyasa, tsaro da huldolin ƙasa da ƙasa na Iran kamar yadda ake yi a zamanin Pahlavi. Ainihin dalilin ƙiyayyarsu shine wannan, sauran maganganunsu kamar 'yancin ɗan adam magana ce mara amfani."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: "Al'ummar Iran ta tsaya da ƙarfi, a gaban sha'awar Amurka, ta tsaya kuma za ta ci gaba da tsayawa, kuma za ta sa su yanke ƙauna daga yaudara da cutarwa."
Da yake yin ishara da barazanar Amurkawa game da yaƙi da amfani da wannan jirgin sama, ya ce: "Wadannan maganganun ba sababbi ba ne kuma a baya ma sau da yawa suna yin barazana cewa duk zaɓuɓɓukan suna kan tebur; yanzu ma wannan mutumin yana ci gaba da yin iƙirari irin wannan cewa mun kawo jirgin ruwa."
Hazrat Ayatollah Khamenei ya kara da cewa: "Ba ya kamata a tsoratar da al'ummar Iran da waɗannan maganganun; waɗannan abubuwan ba zasu taba yi wa al'ummar Iran tasiri ba. Lalle ne mu ba masu farawa ba ne kuma ba ma son yin zalunci da kai hari ga kowa, amma al'ummar Iran za ta yi wa wanda ya yi sha'awa kuma yana so ya kai hari da cutarwa, naushi mai karfi."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara jaddada cewa: "Lalle ne wannan ma Amurka su sani cewa idan wannan karon suka kaddamar da yaki, wannan yaki zai zama yakin yanki."
Your Comment