Tuesday 27 January 2026 - 20:35
Idan Aka Cutar da Iran, Duniyar Musulunci za ta fi Cutuwa 

Hauza/Maulavi Ibrahim Abdallah a wata ganawa da ya yi da mai ba da shawara kan al'adu na Iran a kasar Sri Lanka ya ce: "Mun yi imani da cewa a duniya da muke ciki da kuma a tsakanin al'ummar musulmi Iran ita kadai ce mai goyon bayan musulmi da bukatunsu, don haka wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka kan al'ummar Iran.

A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, biyo bayan makircin makiya juyin musulunci na kasar Iran na haifar da hargitsi da fitina a kasar Iran, Maulavi Ibrahim Abdallah, shugaba da wani gungun mambobin kungiyar Sufaye ta kasar Sri Lanka, a wata ganawa da Ali Kebariyaizadeh mashawarcin al'adun kasar Iran, sun bayyana goyon bayansu ga al'ummar Iran da juyin juya halin Musulunci da Jagoran juyin juya halin Musulunci.

A cikin wannan taro da aka gudanar a yayin taron shawarwarin al'adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Sri Lanka, Maulavi Ibrahim Abdullah ya yaba da tsayin dakan da al'ummar Iran suka yi kan makirce-makircen makiya juyin juya halin Musulunci da kuma hikimar jagoranci inda ya ce: "A irin wannan yanayi wajibi ne musulmin duniya su kasance tare ta hanyar ajiye sabanin da ke tsakaninsu a gefe da kuma rashin barin Amurka da Isra'ila su cimma manufofin da suka sa a gaba na jefa sabani a tsakanin kasashen duniya masu yanci."

Shugaban kungiyar Sufaye ta kasar Sri Lanka ya bayyana cewa, idan aka cutar da Iran, to lallai duniyar Musulunci za ta fi fuskantar mummunar illa, yana mai cewa: "Mun yi imani da cewa a duniya da muke ciki da kuma a cikin al'ummar musulmi, Iran ita kadai ce ta kasance mai goyon bayan musulmi da muradunsu, don haka wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka kan al'ummar Iran."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha