A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Ofishin Yada Labaran Hauza, kungiyar malaman Ahlul-baiti ta kasar Turkiyya a birnin Istanbul ta fitar da wata sanarwa, yayin da ta jaddada cewa zalunci da girman kai yana hannun Amurka da gwamnatin yahudawan sahyoniya, sannan kuma ta bayyana gwagwarmaya da muƙawama karkashin jagorancin Imam Khamene'i a matsayin wani sashe na farko wajen tabbatar da adalci a duniya.
A cikin wannan bayani, malaman Ahlul-baiti na kasar Turkiyya sun kuma gargadi ma'abota girman kan cewa abubuwa masu tsarki na Musulunci da kuma matsayi mai girma na wilaya cikakken jan layi ne kuma mai matukar muhimmanci, kuma duk wani rashin mutunta wannan shaksiyya to zai haifar da mummunan sakamako ga masu wuce gona da iri.
Cikakken bayanin wannan sako shi ne kamar haka:
Da sunan Allah, Mai rahama
A yau, bil'adama, musamman ma duniyar Musulunci, na wucewa ta daya daga cikin jujjuyawar tarihi masu muhimmanci. Iyakoki tsakanin gaskiya da bata sun wuce Gabas ta Tsakiya sun bayyana kamar haske a duk fadin duniya, kuma wadannan rundunonin guda biyu sun ja layi ga juna.
A fili yake ga duk mai hankali da tunani cewa zalunci da girman kai suna hannun Shaidan mai girma, Amurka da shegiyar 'yarsa, gwamnatin sahyoniyawan ƴan mamaya. A daya hannun kuma, fagen muƙawama a karkashin jagoranci ma'abocin hikima Imam Khamenei ya samu ci gaba a matsayin sahun gaba wajen tabbatar da adalci da 'yantar da wadanda ake zalunta.
A wannan lokaci mai muhimmanci, jajircewa wajen yakar azzalumai, da taimakon wadanda ake zalunta, wajibi ne na addini da na bil'adama a kan dukkanin 'yantattun mutane na duniya.
Don haka muna sake yin kira da cewa daga Falasdinu zuwa Yaman, daga Lebanon da Siriya zuwa Myanmar da Venezuela, za mu ci gaba da kasancewa masu goyon baya kuma tare da wadanda ake zalunta a duniya.
Muna gargadin ma'abota girman kai cewa tsarkakan abubuwan Musulunci da kuma jagorancin addini, wanda a yau mai rike da tutar shi ne Ayatullah Imam Khamene'i, su ne cikakken jajayen layinmu. Idan masu girman kai suka bayyana ko da kwayar zarra daga zuciyarsu game da yin ta'ada, to za su fuskanci guguwar fushi mai tsanani da za ta yi musu mummunar barna da sakamako mara misaltuwa.
Muna addu'ar samun nasara ta karshe ga rundunar gaskiya da kuma hadin kan al'ummar musulmi daga Allah madaukaki.
Kungiyar Malamai ta Ahlul-Baiti ta Turkiyya- Istanbul
Your Comment