Marziye Hashemi, sakatariyar bikin fina-finai na Ammar karo na 16, a wata hira da ta yi da wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza a birnin Tehran, yayin da take ishara da sauyin mahangar siyasar Amurka, ta bayyana cewa: "A baya, a Jamhuriyar Musulunci ta Iran kawai ake rera taken "Mutuwa ga Amurka", amma a yau ana jin wannan taken "Mutuwa ga Amurka", a duk fadin duniya sannan har a cikin kasar Amurka ana kona tutar ta."
Ta kara da cewa: "Al'ummar duniya sun farka daga barcin da suke yi, sun fahimci wanene azzalumi na hakika. A yau, hatta jama’ar Amurka sun fahimci cewa idan suka ce “mutuwa ga Amurka”, suna nufin azzaluman manufofin hukumomin mulkin mallaka na Amurka ne; Manufofin da ke son bautar da sauran al'ummomi."
Da take bayyana cewa tana alfahari da kasancewarta a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hashemi ta bayyana cewa: "Ina alfahari da kasancewata a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma ina fatan za mu shaida halakar Amurka da bullowar Imam Wali Asr (AS)."
Sakatariyar bikin fina-finai na Ammar karo na 16, da take martani kan cin mutunci da kalaman batanci da shugaban kasar Amurka ya yi wa Jagoran juyin juya hali, ta bayyana cewa: "Trump ya tafka kuskure. Kada ya bari kazamin bakinsa ya yi magana kan matsayin Jagora."
Your Comment