A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Sheikh Abdullah al-Daqaq babban malamin juyin juya halin kasar Bahrain ya yi Allah wadai da barazanar da shugaban kasar Amurka ya yi wa Imam Khamenei, yana mai kallon wadannan kalamai a matsayin keta ka'idojin diflomasiyya a fili, sannan ya yi gargadin illar da ke tattare da hadari da rashin tabbas a matakin yanki da ma duniya baki daya.
Haka nan kuma yayin da yake jaddada matsayin addini da ruhi na Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: "Ayatullah Khamenei ba wai kawai shugaba ne na siyasa ba, marja'i ne mai girma da tasiri a duniyar musulmi, wanda miliyoyin al'ummar kasashe daban-daban suke bi da kuma koyi da shi."
Ya kara da cewa: "Duk wata barazana ko kai hari kan wannan matsayi na addini da ruhi na iya haifar da tarzoma mai yaduwa da sakamako mai hadari kuma maras tabbas.
Wannan malamin juyin juya halin na kasar Bahrain ya bayyana barazanar da ake yi wa jagoran juyin juya halin Musulunci a matsayin wani aiki na tunzura jama'a da rashin daukar nauyi inda ya ce: "Irin wadannan halaye ba wai kawai suna barazana ga tsaron yankin ba ne, har ma suna iya haifar da sakamako da ya wuce iyakokin kasa."
A karshe Sheik Al-Daqaq ya jaddada cewa: "rashin mutunta Maraji'an addini masu girma a fili karara saba ka'idojin diflomasiyya da zaman tare ne a duniya, don haka ya kamata al'ummar duniya su san illar da irin wadannan abubuwan za su haifar."
Your Comment