Wednesday 21 January 2026 - 23:36
Al'ummar Pakistan Sun Fito kan Tituna Don Goyon Bayan Iran da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

Hauza/An gudanar da gagarumin zanga-zangar nuna goyon baya ga Jagoran juyin juya halin Musulunci a yankin Gilgit-Baltistan na kasar Pakistan.

Sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da gagarumin zanga-zangar nuna goyon baya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma yin Allah wadai da masu tayar da kayar baya yahudawan sahyoniya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yankin Gilgit-Baltistan na kasar Pakistan, inda malamai da jama'a daga ko'ina cikin yankin suka halarta.

Mahalarta wannan muzaharar dai suna rike da hotuna da allunan Imam Khumaini (RA) da Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma Shahid Sayyid Nasrullah da sauran shahidai.

A yayin da mahalartan suka bayyana goyon bayansu ga juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma jagoran juyin juya halin Musulunci, mahalarta taron sun rera taken "Mutuwa ga Amurka" da "Mutuwa ga Isra'ila" tare da bayyana goyon bayansu ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da al'ummarta.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha