Rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayyana cewa, Sayyid Jafar Husaini a cikin littafin "Sanin Nahjul Balaghar Imam Ali da amsa wasu shubuhohi", ya yi ishara da dalilan jan hankalin Nahjul Balagha inda ya rubuta:
Mabiya Ahlus-Sunnah, malaman Shi’a, sauran masana Musulunci, malamai da masana Kiristoci, da dukkan waɗanda suka yi hulɗa da Nahjul Balagha kuma suka yi nazarin sa da kyau, sun yi magana ba tare da banbanci ba game da ƙaƙƙarfan jan hankali na Nahjul Balagha, kuma sun samu kansu ƙarƙashin tasiri da ikon sa.
Wannan jan hankali da ƙaƙƙarfar lallashi da ake ji a cikin huɗubobi, wasiƙu, da gajerun kalaman Imam Ali (a.s), shi ne babban kwarin gwiwa ga rukunin masana wajen yin sharhin Nahjul Balagha ko rubuta littattafai da maƙalu game da halayen Ali (a.s).
Kuma a nan za mu kawo muhimman dalilai bayyanannu na wannan jan hankali:
1- Jan hankali na ɗabi'a da na sanin Allah (Irfani) na Nahjul Balagha suna da yadda suke shayar da rayukan da suke jin ƙishirwa da ruwan sanyin ilimi. A cikin huɗubobi da dama, ciki har da huɗuba ta farko da huɗuba ta "91" (Huɗubar Ashbah), lokacin da ake magana kan sanin Allah da jan hankali na kyawawan siffofinSa da girmanSa, kalaman sa suna yin sama yadda mai karatu yake jin kamar yana kan fiffiken mala'iku ne, kuma yana hawa zuwa wurare mafi nisa waɗanda tunanin ɗan adam ba zai iya wuce su ba. A lokacin ne surar wani babban masanin falsafar Allah take bayyana a gaban sa, wanda shekaru masu yawa ya kasance yana magana kan tauhidi, kuma yana bayyana Allah yadda mutum yake ganin sa da idon zuciya a ko'ina; a cikin sammai, a ƙasa, da kuma cikin ransa, sai ransa ya cika da hasken sanin Ubangiji.
2- A cikin Nahjul Balagha, a ko'ina magana ake ta tausayawa gajiyayyu da waɗanda aka zalunta a cikin mutane. Dukkan magana akan yaƙi da zalunci da rashin adalci da zaluncin masu mulki da azzalumai ne. A ko'ina magana ake kan yaɗawa da faɗaɗa adalcin zamantakewa da kawar da kowane irin zalunci da wariya. A ko'ina magana ake kan rabo na adalci da daidaito na baitul-mali da rashin fifita dangi a cikinsa. Har zuwa inda muke karantawa a huɗuba ta "224"[Nahjul Balagha, H:224; S:360; Bugun Darus-Saƙalain-Qom], lokacin da Aqeel (ɗan uwan Imam) ya nemi mudu ɗaya (kilogiram 3) na alkama daga baitul-mali fiye da haƙƙinsa, ya sami amsa da ƙarfe mai zafi! Amirul Muminina Ali (a.s) yana yin gargaɗi cewa; duk inda aka samu tarin ni'imomi da aka tara, to akwai haƙƙoƙin da aka tauye a gefensa: "Ban ga wata ni'ima mai yawa ba, face a gefenta akwai haƙƙin da aka tozarta."
3- Nahjul Balagha a ko'ina yana tafiya ne a tafarkin 'yantar da ɗan adam daga sarkar bautar sha'awar zuciya, wadda take janyo masa ƙasƙanci da rashin sa'a, da kuma bautar azzalumai masu mulki da masu hannu da shuni masu yawan buƙata. Yana amfani da kowace dama don wannan manufa mai tsarki. A cikin huɗubar Shaƙshaƙiyyah (Huɗuba ta 3), yana gargaɗin cewa kada a nuna rauni ko kaɗan wajen dawo da ruhin 'yanci da daidaito da adalci, domin saboda wannan al'amari ne ya amshi babban matsayi na gwamnati.
4- "Nahjul Balagha" da kalaman Ali (a.s) suna shiga can cikin zurfin ran masu neman gaskiya, kuma suna haifar da tasirin da ba za a iya siffanta shi ba. Kamar "Hammam", wannan mutumin mai yawan ibada da sanin Allah, wanda ya nemi sanin matsayin halayen masu tsoron Allah daga shugaban masu takawa. Da farko Imam ya ƙi, amma shi ya nace. Imam Ali (a.s) ya faɗi wannan huɗuba mai ban mamaki kuma marar tamka, inda ya lissafa masa siffofi sama da ɗari na masu tsoron Allah. Bayan ya ji wannan huɗubar, ya saki wata ƙara ya faɗi ƙasa ya rasu.[Nahjul Balagha, H:196 "Huɗubar Muttaƙiyn"; S:313-317, Bugun Darus-Saƙalain-Qom]
Irin wannan tasiri na magana wani abu ne da babu irinsa a tarihi. A sannan Imam Ali (a.s) ya ce: "Wallahi na kasance na ji tsoron hakan gare shi - sannan ya ce - Shin haka wa'azi mai ratsa jiki yake yi ga waɗanda suka cancanta?" Shi kansa Sayyid Radhi, wanda yake ɗaya daga cikin mashahuran malaman adabin Larabci, bayan ya kawo wasu huɗubobin, yana da wasu bayanai da suke nuna yadda mutane suke fita daga hayyacinsu da jan hankali yayin jin waɗannan huɗubobin, ko kuma yadda shi kansa ya kasance ƙarƙashin tasirin ƙaƙƙarfan jan hankali na kalaman.
Daga ciki:
A) A ƙarƙashin huɗuba ta 83 (wadda ake kira "Huɗubar Garra’u"), marubucin ya kawo cewa: "An ruwaito cewa, lokacin da Imam Ali (a.s) ya karanta wannan huɗubar, jiki ya girgiza ya yi tsumu-tsumu, idanu suka zubar da hawaye, zukata kuma suka shiga tsoro da bugawa."[Nahjul Balagha, H:83, S:99-111 Bugun Darus-Saƙalain-Qom]
B) A ƙarƙashin huɗuba ta 289, ya ce: "Idan akwai wata magana da za ta jawo mutane zuwa ga guje wa duniya (zuhudu) kuma ta tura su zuwa ga yin aiki don lahira, to wannan maganar ce; ita ce take iya yanke sha'awar mutum ga dogon buri, kuma ta kunna tartsatsin farkawa, wayewa, da kyamar ayyukan assha a cikin zuciyarsa."
Ibn Abil Hadid al-Mu'utazili, a cikin sharhin huɗuba ta "109", yana cewa: "Tasiri da jan hankali na wannan huɗubar ya kai matsayin da idan aka karanta ta ga mutumin da ba shi da addini (mulhidi), wanda ya ƙuduri niyyar musanta ranar tashin ƙiyama da dukkan ƙarfinsa, to ƙarfinsa zai ruguje, zuciyarsa za ta shiga firgici, sannan kuma kudurinsa na musanta hakan zai yi rauni, har ma tushen akidarsa ya fara girgiza."
Sannan ya ci gaba da cewa: "Saboda haka, Allah Maɗaukaki ya saka wa mai wannan magana (Imam Ali) da mafi alherin sakamako saboda wannan hidima da ya yi wa Musulunci; mafi kyawun sakamakon da Ya taɓa ba wa wani waliyi daga cikin waliyansa. Domin kuwa yadda ya taimaki Musulunci abin sha'awa ne; wani lokacin da hannunsa da takobinsa, wani lokacin da harshensa da bayaninsa, wani lokacin kuma da zuciyarsa da tunaninsa. Haka ne, shi ne 'Sayyidul Mujahidin' (shugaban masu jihadi), 'Ablaghul Mowa'izin' (mafi hikimar masu wa'azi), 'Ra'isul Fuqaha wal Mufassirin' (shugaban malaman fikihu da masu tafsiri), kuma 'Imamu Ahlil Adli wal Muwahhidin' (shugaban ma'abuta adalci da masu kadaita Allah)."[Sharhin Nahjul Balagha, Ibn Abil Hadid, J:7, S:202]
Your Comment