Monday 1 December 2025 - 07:02
Shin sabani tsakanin bangarori biyu ni’ima ne ko fitina?

Hauza/ Ba dukkan sabani cikin al’umma ake ɗauka a matsayin abu maras kyau ba. Wasu sabanin, musamman irin waɗanda ke cikin siyasa, kan zama turbar cigaba; su zafafa fafatawa, su kuma ceci al’umma daga durƙushewa. Amma sabanin da ke rushewa ko hana juna cigaba kuwa, fitina ne da ke haifar da tashin hankali da koma baya.

Acewar Kafar yada labarai ta Hauza, A cikin ɗaya daga cikin rubuce-rubucensa, Shahid Ustaz Murtada Mutahhari ya tabo batun “sabanin da ke faruwa tsakanin kungiyoyi da bangarori biyu a cikin al’umma”.

Mutahhari ya bayyana cewa sabanin da ke faruwa a al'umma wasu lokuta suna da tushe na hankali. Misali, idan wata al’umma ta ƙunshi kungiyohi biyu da bangarori na siyasa masu tsare-tsaren da suka bambanta, dole ne a ce suna tsaye ne a gaban juna ta fuskar ra’ayi. Ta yadda za'a ga dayan bangren yana suka ga ayyukan ɗayan bangaren, ɗayan bangaren ma yana sukar na ɗayan. Wannan irin yanayi yakan sa duka bangarorin biyu su nemi yin gaba - don inganta aiyukan su.

Idan irin wannan sabanin bai wanzu ba, kuma kowa ya tsaya kan tunani guda ɗaya, al’umma za ta zama tamkar ruwa da yake tsayewuri guda – motsinta zai yi rauni sosai, har ma ya kai ga durƙushewar mu’amalar zamantakewa. Haka kuma Akwai sabani irin na gasa: mutum na gudu yana neman gaba, wani na kokarin yin gaba da shi – ire - iren wannan sabani rahama ne.

Amma akwai sabanin da mutum yana ƙoƙarin ɗaga ƙafa ya matsa gaba, sai wani ya makale a bayansa yana hana shi cigaba. Wannan kuwa fitina ce, ba ni’ima ba. Ire - iren wannan nau’in sabani da ya yi kama da tashin hankali, wato sabanin da ke soke aikin juna, shi wannan kam fitina ne.

An dibo daga: Littafin “Sanin Allah daga Mahangar Alƙur’ani”, shafuffuka 190–191.


Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha