Saturday 7 February 2026 - 15:21
Harin Ta'addanci A Sallar Juma'a Ta Shi'a A Islamabad, Pakistan Ya Yi Sanadiyyar Shahada da Jikkata da Dama

Hauza/ A sakamakon wani harin kunar bakin wake yayin gudanar da sallar juma'a a Husainiyya da Masallacin «Khadijatul-Kubra» da ke birnin Islamabad na Pakistan, akalla masallata 31 ne suka yi shahada, kuma sama da 169 suka jikkata.

A wani rahoto daga sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza a birnin Islamabad na Pakistan, wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa a yayin gudanar da sallar juma'a a Husayniya da Masallacin «Khadijatul-Kubra». A bisa ga sabbin rahotanni, a wannan lamarin akalla masallata 31 ne suka yi shahada, kuma sama da 169 suka jikkata.

Bisa ga bayanan da shaidun gani da ido suka bayar, maharin ya fara harbin jami'an tsaron da ke kofa tare da jikkata su. Daga nan sai ya nufe masallacin, kuma a bakin kofar, yayin da masu ibada suke cikin gudanar da raka'a ta biyu ta sallar juma'a, sai ya tayar da bam din da ke jikinsa.

Bayan fashewar bam din, jami'an 'yan sanda, kungiyoyin tsaro, da kuma tawagar kwance bom marasa fashewa sun garzayo wurin nan take kuma suka killace yankin. A yayin da ake wannan halin, a asibitoci daban-daban na babban birnin, ciki har da Polyclinic, PIMS, da asibitin CDA, sun ayyana yanayi na gaggawa, kuma an soke hutun ma'aikatan kiwon lafiya.

Bugu da kari, asibitin Polyclinic na Islamabad ya fitar da sanarwa yana neman jama'a su bada gudunmawar jini, domin ma'aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa domin ceto rayukan wadanda suka jikkata, ana matukar buƙatar jini.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha