Monday 26 January 2026 - 22:17
Fahimtar Sabuwar Duniya da Sabbin Guguwowi Masu Tasowa Shi Ne Babban Aikin Mu / Makarantun Hauza; Jagororin Tunanin Musulunci a Wannan Zamanin 

Hauza/Ayatullah A'arafi yayin bayyana cewa cibiyoyin addini suna da babban nauyi a wuyansu, ya bayyana cewa: " Farko kuma asalin aikinmu shi ne fahimtar sabuwar duniya da guguwowi masu tasowa, domin ba tare da wannan ilimin ba, ba za a iya daukar wani mataki mai inganci ba.

Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayar da rahoton cewa, Ayatullah Alireza A'arafi a ganawarsa da darakta da membobin cibiyar kula da bincike na makarantun Hauza, yayin da yake ishara da falaloli da albarkoki na musamman na watan Sha'aban, ya ce: "Allah madaukakin sarki ya ba wa dukkan muminai nasarar cin gajiyar falalar wannan wata na neman kusanci zuwa ga Allah da daukar matakai mafi girma a fagen bunkasa ilimin addini da kuma ci gaban Iran."

Ayatullah A'arafi, yayin da yake ishara da irin gagarumin ci gaba da aka samu a fagen kasa da kasa, ya bayyana cewa: "Sabuwar duniya da kuma yanayin da muke ciki a cikin shekaru biyun da suka gabata, ta samu sabani na asali daga abubuwan da suka gabata, kuma a cikin zuciyar wadannan ci gaban akwai damammaki masu girma da kuma barazana mai tsanani, wadanda suke bukatar nazari na tsanaki daga makarantun Hauza da dukkanin bangarorin da suka dace.

Yayin da yake bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a gano dama, kalubale, barazana da manufa a halin da ake ciki, memba na majalisar koli ta Hauza ya tattauna tare da nazari kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, inda ya ce: "A farkon abubuwan da suka faru shekaru biyu da suka gabata, a cikin nazarce-nazarcen da na gabatar a da'irori daban-daban, na jaddada cewa, wata sabuwar guguwa ta afku wacce ta bambanta da dukkan guguwar da suka gabata, kuma mai nauyi sosai; Hanyar da za ta ci gaba. Don haka dole ne masu fikirar juyin juya halin Musulunci, Hauza da cibiyoyin addini su zama cikin kammalallen shiri."

Ayatullah A'arafi yayin da yake jaddada cewa abubuwan da suke faruwa a halin yanzu da suka hada da yaki da tarzoma da sauran batutuwa na asasi, ba za a iya kwatanta su da zamanin da suka gabata ba, ya bayyana cewa: "Wadannan yanayi sun sha bamban da dukkanin zamanin da suka gabata kuma suna da nauyi matuka. Ni, na kasance wanda ya tsunduma cikin lamurran juyin juya halin Musulunci tun ina matashi, ina shaidawa cewa halin da ake ciki ya sha bamban da dukkan lokutan da suka gabata. Tabbas, har yanzu ina fatan samun damammaki masu mai girma tare da wadannan barazanar, amma ban raina yawan barazanarsu da kalubale ba."

Shugaban makarantun Hauzar a ci gaba da bayyana cewa cibiyar addini tana da babban nauyi matuka a wuyanta, ya ankarar cewa: "Muna da manufa ta aikin addini, kuma ya kamata makarantun Hausa su taka rawa a matsayin jagora na tunani na Musulunci da juyin juya hali a wannan zamani."

Memba a majalisar shari'a na Majalisar ƙoli ya jaddada cewa: "Aikinmu na farko kuma na asali shi ne sanin wannan sabuwar duniya da guguwowi masu tasowa; Domin ba tare da wannan ilimin ba, ba zai yiwu a iya daukar wani mataki mai tasiri ba."

Ayatullah A'arafi yayin da yake jaddada muhimmancin ci gaba da alaka tsakanin cibiyoyin addini da malamai da kuma al'umma, ya bayyana cewa: "Makarantun Hauza da cibiyoyin malamai a halin da ake ciki a halin yanzu suna fuskantar damammaki na musamman na tarihi albarkacin juyin juya halin Musulunci, da kuma kalubale da matsaloli da suke barazana ga wannan cibiya."

Ya kara da cewa: "Yin nazari kan wannan batu da samar da mafita a gare shi lamari ne mai matukar muhimmanci da ya kamata cibiyoyin bincike su yi la'akari da su sosai. Sai dai matakan da aka dauka ya zuwa yanzu ba su isa ba kuma akwai bukatar yin aiki dalla-dalla kuma zurfafa da suka hada da matakin al'umma musamman ma matasa, da kuma a matakin manyan masana da jami'o'i. Baya ga cikin kasar nan, wajibi ne a ga wadanne irin ra’ayoyi ne ma'abota addini ke da shi dangane da mu da kuma irin batutuwan da ke cikin zukatansu."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha