A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, rubutun sakon ta'aziyyar Ayatullah A'arafi ga shi kamar haka:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
Rashin babban Mallami mai daraja Ayatullah Hajj Sayyid Hadi Sistaniy bayan rayuwa mai cike da kokari da mujahadar ilimi da aiki abu ne da ya bar tarihi.
Ina mika sakon ta'aziyyata na rashin wannan Mallami mai daraja ga mai girma babban marja'i, Ayatullah Sayyid Ali Sistaniy, sauran iyalan da ya bari, gidajen da rashin ya shafa da kuma manyan dalibansa. Ina rokon Allah (SWT) ya gafarta masa kuma ya daukaka makwancinsa. Ina kuma rokon Allah ya bawa iyalansa ladan juriya da hakurin wannan babban rashi.
Alireza A'arafi
Shugaban Makarantun Hauza
Your Comment