Monday 19 January 2026 - 21:18
Sakon Ta'aziyyar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ga Ayatullahil Uzma Sistaniy

Hauza/ Mai girma Ayatullah Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wani sako, ya mika ta'aziyyarsa kan rasuwar dan uwan mai girma Ayatullah Sistaniy.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, mai girma Ayatullah Khamene'i a cikin wani sako ya mika ta'aziyyarsa na rasuwar dan uwan Ayatullah Sistaniy.

Cikakken sakon ta'aziyyar ta Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ga ta kamar haka:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Mai girma Ayatullah Sistaniy (DB)

Ina mika maka sakon ta'aziyyata na rasuwar dan uwanka mai girma. Ina rokon Allah (SWT) ya gafarta masa sannan ya sada shi da kakanninsa masu girma, Ahlul Bayt (AS).

Sayyid Ali Khamene'i

18 ga Janairu, 2026

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha