Tuesday 6 January 2026 - 01:46
Gagarumar Muzaharar Murnar Haihuwar Amirul Muminin (AS) a Birnin Varanasi na Kasar Indiya

Hauza/ Daidai da lokacin zagayowar ranar haihuwar Amirul Muminin Imam Ali (AS), an gudanar da wani gagarumin tattaki a birnin Varanasi (Benares) na kasar Indiya, wanda ya nuna matukar soyayya ga Imam Ali da kuma zaman tare cikin lumana tsakanin mabiya addinai daban-daban.

A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, domin murnar wannan rana mai albarka, dubban mutane ne daga sassa daban-daban na al'umma suka taru a birnin Varanasi domin gudanar da wannan taro na murna.

Masu halartar tattakin sun rika rera taken "Haidar, Haidar" da "Ya Ali", inda suka bayyana matukar kaunarsu ga Amirul Muminin (AS), wanda hakan ya cika sararin birnin da ambaton sunan sarkin muminai. Wannan biki ya zama wata bayyananniyar shaida ta zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai a birnin Varanasi. Mabiya addinai da mazhabobi daban-daban sun tsaya a gefen hanyar da masu tattakin ke bi, suna yayyafa musu furanni, tare da raba ruwa da alawa (sweet) ga mahalarta taron. Wadannan ayyuka sun samar da kyawawan hotuna na hadin kai, soyayya, da girmama juna tsakanin al'ummar birnin.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha