A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, ga cikakken sakon Ayatullah Nuri Hamadani wanda aka karanta a daren jiya a taron rufe bikin da aka gudanar a makarantar Imam Kazim (A.S) da ke birnin Qum:
Bismillahir Rahmanir Rahim
“Ba mu aika wani Manzo ba face da yaren mutanensa, domin ya bayyana musu (sakonnin Ubangiji)...” (Suratu Ibrahim, Aya ta 4)
Ina mika gaisuwa da fatan alheri ga mahalarta da masu sauraron wannan biki na rufe gasar fasaha ta "Honare Asemani" karo na goma.
Yanzu da muke gab da karkare wannan biki na goma, muna jinjinawa wannan gagarumin taron mai tasiri a fagen wa'azi na makarantun addini (Hauza). Muna mika godiya da yabo ga shugaban makarantun addini, jami’an cibiyoyin fasaha da na Hauza, ma’aikata da masu shirya wannan biki, da kuma daliban addini (Daliban Hauza) masu fasaha wadanda suka kara armashin wannan biki da gudunmawarsu.
A wannan zamani na fasahar sadarwa (technology), mayar da hankali ga kayayyakin wa'azi na zamani, musamman ta hanyar yin amfani da "Fasaha madaukakiya", na iya zama wani mataki mai tasiri wajen yada tunani na kadaita Allah da wahayi. Hakan zai taimaka wajen isar da kokari da nasarorin ilimi na malaman Hauzah ga al'ummar Musulmi cikin salon zamani, tare da shayar da masu kishirwar ilimin mazhabar Shi'a.
Ayoyi masu haske na Alkur'ani mai girma da ruwayoyin Ahlul-Baiti (A.S), su da kansu suna daya daga cikin manyan ayyukan fasaha wadanda tun farkon aiko Manzon Allah (S.A.W.A) suka kasance harshe mai bayyana manufofin kadaita Allah, kuma sun yi nasarar isar da koyarwar Ubangiji zuwa ga rayukan mutane ta hanya mafi kyau.
Kulawa da amfani da fasaha da addinin Musulunci ya yi, ya sanya manyan malamai da masana na makarantun addini karkata zuwa ga fasaha madaukakiya. A tsawon tarihin ilimi da fikihu, mun shaida ayyukan fasaha masu daraja da malamai da daliban addini suka samar.
Lallai, ba da muhimmanci na musamman da Cibiyar Gudanarwar Hauza take ba wa "Fasaha" abu ne mai albarka da muhimmanci, kuma hakan busharar kyakkyawar makoma ce a fagen wa'azi na zamani.
Bikin "Honare Asemani", wanda ke nuna tasirin halartar daliban Hauza masu fasaha a fagen wa'azi na zamani, shi kansa wani babban mataki ne na dabara wajen isar da sakon Hauza. Kasancewar a wannan karon an hada da sashe na musamman kan "Wa'azi na zamani da kuma Artificial Intelligence 'AI', hakan na nuni da zurfin hangen nesa na mahukuntan Hauza game da wa'azi na zamani.
Ina yi wa masu shirya wannan biki fatan nasara fiye da na baya, ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya cika zuciyoyinmu da hasken ilimin addini, sannan Ya sanya ayyukanmu na al'adu, fasaha, da wa'azi su zama shimfida ga bayyanar mai jiran gado, Imam al-Mahdi (Ruhina su zama fansa gare shi).
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh
Qum – Hossein Nuri Hamadani
Your Comment