Wednesday 24 December 2025 - 15:58
Faɗaɗa Darussan Bincike na Koli (Kharij) a Fannin Ilimin Kalam na Daya Daga Cikin Buƙatu na Gaggawa / Muhimmancin Kasancewa a Fagen Ilimin Duniya

Hauza/Shugaban makarantun addini (Hauza )na ƙasar Iran, yayin da yake jaddada muhimmancin daukaka matsayin ilimin Kalam na Musulunci ya kai matsayin ijtihadi na Fiqhu da Usul, ya yi kira da a sake fasalin litattafai, faɗaɗa darussan Kharij na ilimin Kalam, bayar da amshoshi masu gamsarwa ga shubuhohi (shakku) na zamani, da kuma kasancewa mai ma'ana a fagage na fuskantar ƙalubale na tunani da ilimi a duniyar yau.

A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun addini na ƙasar, ya bayyana hakan ne a zama na takwas na tattaunawa kan ra'ayoyin yadda za a tabbatar da sakon "Hauza mai jagoranci da cigaba". Wannan taro dai ya gudana ne a ofishin gudanarwar makarantun addini (Hauza), ƙarƙashin shirye-shiryen mataimakin shugaban sashin ilimi na Hauza tare da haɗin gwiwar cibiyoyin bincike na ilimin Kalam na Musulunci.

Yayin da yake taya murna ga zagayowar darajoji na watan Rajab da kuma murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Muhammad Baqir (AS), Ayatullah A'arafi ya bayyana waɗannan watanni a matsayin masu matuƙar tasiri wajen daukaka ruhi da kyawawan halaye. Ya kuma bayyana cewa: "Ɗaya daga cikin muhimman fuskoki na koyarwar Musulunci shi ne matsayin addu'o'i da ziyara wajen karfafa da kuma zana tushen akidu; babban sashe na iliminmu na akida yana bayyana ne a cikin madubin addu'o'i da ziyara."

Shugaban makarantun addini (Hauza), yayin da yake jinjinawa ƙoƙarin malaman fannin, ya jaddada mahimmancin ba da fifiko ga ijtihadi na hankali (rational ijtihad) a cikin ilimin akida, faɗaɗa darussan Kharij na ilimin Kalam, sake fasalin litattafai, kula da sauye-sauyen ilimi na duniya, da kuma halartar Hauza cikin fagen tunani na duniya baki ɗaya.

Ayatullah A'arafi, yayin da yake godiya ga mataimakin shugaban sashin ilimi na Hauza da kuma duk waɗanda suka shirya wannan zama, ya bayyana fatan cewa waɗannan tarukan na tattaunawa da musayar ra'ayi za su dore, sannan ta hanyar haɗin gwiwar sassa daban-daban na Hauza, a samu damar cike gurbi da kuma zurfafa mahuwarai na ilimin Kalam.

Ya nuna godiyarsa ga ayyuka masu faɗi da aka gudanar a fannonin ilimi, bincike, fashin baki, yaɗawa, da kuma samar da tattaunawa (discourse) kan mahuwarai na akida da ilimin Kalam. Ya bayyana cewa: "Wani babban sashe na waɗannan ayyukan ana gudanar da su ne a cikin Hauza, musamman ma ta hanyar ƙoƙarin manyan malamai, waɗanda duka sun cancanci godiya da yabo."

Ayatullah A'arafi, yayin da yake nuni ga muhimmancin abubuwan da suka shafi mahuwarai na akida, ya bayyana cewa: "Ba tare da shakka ba, fifiko na farko na Hauza ya kasance gano gaskiya da ijtihadi cikakke, mai ma'ana, na hankali, kuma ingantacce a fannin ilimomin asasi da na akida. Kuma a lokaci guda, ya kamata a bi sahun yaɗawa, fashin baki, kore shubuhohi, da fuskantar hare-hare na tunani a matsayin fifiko na farko."

Shugaban makarantun addini na ƙasar ya ci gaba da bayanin tafarkin gudanarwa na Hauza a shekarun baya-bayan nan inda ya ce: "Duk da cikas, ƙarancin ababen more rayuwa, da matsaloli na zahiri na ayyukan Hauza, an yi ƙoƙarin ganin an tsara motsin Hauza bisa wani tsari na asali, tare da la'akari da buƙatun Jagora, manyan Maraji'ai, da kuma babban rukunin ɗalibai da malaman Hauza. Koda yake akwai tazara mai yawa kafin a kai ga matsayin da ake buƙata, amma an yi ayyuka masu yawa a fannin tsare-tsare na gabaɗaya, gano fannoni (subject-recognition), samar da kundaye (documents), da kuma tsara bishiyar rassa na fannonin ilimi (tree of disciplines)."

Yayin da yake nuni ga haɗin gwiwar kusan mutane dubu ɗaya wajen tsara bishiyar fannonin ilimi na Hauza da kuma kundaye na bai-ɗaya a cikin shekaru biyar da suka gabata, ya jaddada cewa: "Wannan tafarki ya ci gaba duk da wasu suka da aka fuskanta.

A yau, waɗannan kundayen ana kallon su a matsayin tsarin ilimomin Hauza a cibiyoyin ilimi na cikin gida da na waje, koda yake idan aka kwatanta da girman sauye-sauyen tunani da na yawan jama'a a duniyar yau, waɗannan matakan ba su isa ba tukuna."

Ayatullah A'arafi ya yi nuni da aiwatar da manyan ayyuka (projects) sama da guda 100 a fannoni daban-daban, ciki har da tsara fasalin rukunin masu wa'azi (muballigai), tallafawa makarantu, da kuma haɗin gwiwa da hukumomin yaɗa addini da na gwamnati. Ya bayyana cewa: "Koda yake wasu daga cikin waɗannan ayyukan ba sa cikin ayyukan hukuma na gudanarwar Hauza, amma saboda nauyin da ya rataya a wuyanmu na addini da na Hauza, an yi ƙoƙari a waɗannan fannonin."

Yayin da yake nuni ga yanayin rudani na tunani a duniyar yau, ya bayyana cewa ayyukan ilimin Kalam da ake gudanarwa a yanzu ba su taka kara sun karya ba idan aka kwatanta su da yawan shubuhohi da ƙalubale na duniya. Ya ƙara da cewa: "Fannin ilimin Kalam yana buƙatar cikakken shiri (comprehensive program), raba ayyuka cikin tsanaki, da kuma taswira bayyananna don mamaye dukkan fagage na tunani, tun daga sabbin akidun rashin Allah (New Atheism) har zuwa shubuhohi na cikin addini da na ɓangaren ƙungiyoyi (sects)."

Shugaban makarantun addini na ƙasar ya bayyana cewa, faɗaɗa darussan bincike na koli (Kharij) a fannin ilimin Kalam na ɗaya daga cikin buƙatu na gaggawa. Ya jaddada cewa: "Dole ne darasin Kharij na ilimin Kalam ya kai matsayin bincike na Usul ta fuskar nauyin ilimi da hanyoyin bincike. Abin da ake sa rai shine cewa nan ba da jimawa ba, darussan Kharij na ilimin Kalam masu yawa za su kafu a cikin Hauza tare da samar da bincike na matakin ijtihadi."

Mamba a Majalisar Ƙoli ta makarantun addini (Ayatullah A'arafi) ya bayyana cewa, sake fasali da kuma rayar da tsofaffin litattafan ilimin Kalam, Tafsiri, da Falsafa wata babbar dama ce. Ya ce: "Hauza tana da babban gado na ilimi wanda bai kamata a bar shi a gefe ba. Dole ne a ba wa waɗannan litattafai muhimmanci kuma a sake karanta su a matsayin ginshiƙin hankali na gadon Hauza."

Ayatullah A'arafi ya yi nuni da buƙatar tsara matakan karatu mafi girma bayan mataki na huɗu (Level 4), horar da kwararru a fannoni na musamman na ilimin Kalam, da kuma ba da muhimmanci ga samar da asali (identity) ga ilimin Kalam. Ya ƙara da cewa: "Hanyar ilimin Kalam tana da rawar asali wajen bayyana koyarwar addini, kuma dole ne a ƙarfafa ta ta hanyar yin amfani da hikima daga fannin Falsafa, ba tare da mika wuya gare ta ba tare da nazari ba."

Shugaban Hauzar ya bayyana cewa sadarwa mai ma'ana da jami'o'i da kuma kasancewa a fagen ilimi na duniya na ɗaya daga cikin abubuwan da ake buƙata a yau. Ya jaddada cewa: "Dole ne ayyukan ilimi na Hauza su kasance suna da ikon yin tattaunawa da kuma kariya ta hankali (rational defense) a jami'o'in cikin gida da na waje, a coci-coci, da kuma tarukan ilimi na ƙasa da ƙasa."

Shugaban makarantun addini na ƙasar ya bayyana cewa, yana da matuƙar muhimmanci a san ilimomin zamani, falsafar yamma, ilimin sanin ɗan adam (human sciences), da kuma ilimomin asali (basic sciences) waɗanda suke da alaƙa da ilimin addini (theology), musamman ma ilimin fiyzik (physics) da ilimin kimiya na sararin samaniya (cosmology). Ya jaddada cewa: "Yawancin shubuhohi (shakku) na zamani suna samo asali ne daga waɗannan fannoni, kuma ba tare da saninsu mai zurfi ba, ba zai yiwu a bayar da amshoshi ba."

Yayin da yake nuni ga saurin sauye-sauyen fasaha da kuma fasahar nan ta Artificial Intelligence (AI), ya bayyana wannan fanni a matsayin ɗaya daga cikin mafi muhimmancin ƙalubale da kuma damammaki na nan gaba. Ya ce: "Dole ne ilimin addini, falsafa, fiƙihu, ɗabi'u (akhlaq), da kuma shari'a (law) da suka shafi AI su kasance cikin jerin ayyukan Hauza cikin gaggawa; domin kuwa AI ba kawai kayan aiki ba ne, face dai nan ba da jimawa ba zai zama mai taka rawa wajen samar da ilimi da kansa."

A ƙarshe, Ayatullah A'rafi ya jaddada buƙatar tsara ƙa'idodin akida (charters) masu ƙarfi, ba da muhimmanci sosai ga hanyoyin bincike (methodology) a fannin ilimin Kalam, da kuma ƙarfafa tafarkin hankali na ijtihadi. Yayin da yake godiya ga malaman da suka halarta, ya bayyana fatan cewa za a bi sahun dukkan matsalolin da aka tattauna cikin haɗin gwiwa domin su haifar da sakamako na zahiri.

Yana da kyau a sani:

Wannan shi ne zama na takwas na tattaunawa kan ra'ayoyi don aiwatar da saƙon Jagoran Juyin Juya Hali zuwa ga makarantun addini (Hauza), wanda aka keɓe don malaman ilimin Kalam. An gudanar da taron ne da nufin nazarin matsalolin ilimi, koyarwa, da dabarun gudanarwa na wannan fanni, da kuma musayar ra'ayi kan hanyoyin ɗaukaka matsayin ilimin Kalam wajen fuskantar ƙalubale na tunani na zamani. Wannan taro ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban sashin ilimi na makarantun addini (Hauza).
Rahoton ra'ayoyi da shawarwarin malaman da suka gabatar da bayanansu a wannan zama zai fito nan gaba kaɗan.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha