Saturday 20 December 2025 - 22:26
Jagoran Juyin Juya Hali na Damuwa Da Rayuwar Mutane/A yau Filin Daga shi ne Fagen Yada Labarai

Hauza/ Limamin Juma'ar birnin Qom ya bayyana cewa: Jami’ai sun bayyana cewa daya daga cikin manyan damuwar Jagoran juyin juya hali a tarurrukan da yake yi da masu fada a ji, ita ce maganar hauhawar farashi, karuwar farashin kayayyaki, da matsalolin rayuwar al'umma.

A cewar wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Muhammad Sa'idi, a cikin hudubar sallar Juma'a ta ranar 19 ga watan Disamba 2025 da aka gudanar a masallacin Quds da ke Qom, ya bayyana cewa: Imam Ali (AS) yana cewa: "Ka ji tsoron Allah koda kadan ne, kuma ka sanya labule (shamaki) na kunya tsakaninka da Allah koda kuwa siriri ne."
Ya bayyana cewa: "A halin yanzu, mafi muhimmancin fagen adawa da makiya shi ne fagen farfaganda da yada labarai. Fage ne da manufar makiya a cikinsa ita ce mamaye tunani da zukata. Kwarewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna cewa al'ummar Iran a ko da yaushe suna fuskantar matsin lamba na soja, tattalin arziki, al'adu, da na yada labarai, amma Jamhuriyar Musulunci ta sami damar kiyaye 'yancinta da ikon yanke shawara, kuma ta isar da ruhin gwagwarmaya da masu girman kai zuwa ga sauran al'ummomi, ta yadda a yau ba za a iya fahimtar sauye-sauyen yankin ba tare da fahimtar rawar wannan gwagwarmayar ba."
Limamin Juma'ar na Qom ya ci gaba da cewa: "A irin wannan yanayi, fuskantar makiya a fagen yada labarai yana bukatar shirin yaki. Shirin da ba na kariya kawai ba ne, a'a a cikin yakin yada labarai ya kamata a kai hari kan raunanan wuraren makiya tare da sanin dabarunsu daidai. Yakin yada labarai yaki ne na kowa da kowa, kuma kowane mutum ana daukarsa a matsayin mai fafutuka."
Ya bayyana cewa: "Kasancewa ɗan kallo kawai yana nufin yin baya a wannan jihadi na fisabilillahi. A yau makiya sun sanya koyarwar Musulunci, juyin juya halin addini, kamun kai da hijabi, da kunyar maza da matanmu a gaba. Don haka, a wannan yakin kada mu kasance masu kariya kawai, a'a dole ne daukacin al'umma, da jami'ai da mutane, su kai hari ga makiya da dukkan karfinsu, su yanke hannaye da kafafunsu kazamai ta yadda ba zasu sake tunanin cin zarafin Jamhuriyar Musulunci ba."
Wakilin jagora a Qom ya kara da cewa: "Nazarin kalaman Jagoran juyin juya hali ya nuna cewa al'amuran da suka shafi tattalin arziki su ne kan gaba. Jami'ai sun bayyana cewa daya daga cikin manyan damuwar Jagora a tarurrukansa da masu fada a ji ita ce maganar hauhawar farashi, karuwar farashin kayayyaki, da matsalolin rayuwar mutane."
Ya ci gaba da cewa: "Jagoran juyin juya hali ya sha tunatar da manyan jami'an kasar cewa tattalin arziki shi ne abu na farko da kasar ke bukata. Koda yake Jagora yana jaddada ayyukan samar da ababen more rayuwa da suka shafi ci gaban kasa, amma ko da yaushe damuwarsa ita ce, har zuwa lokacin da sakamakon ayyukan more rayuwa zai bayyana, kada a yi sakaci da al'amuran gaggawa na rayuwar mutane kamar tsadar kayayyaki da hauhawar farashi."
Yana mai ishara da farkon watan Rajab, ya ce: "Watan Rajab dama ce ta kusanci ga Allah, tarbiyyar kai, neman taimako, mayar da hankali da addu'a. Watan Rajab da Sha'aban matakin shirye-shirye ne na shiga watan Ramadan. Rajab watan i'itikaf ne na bayin Allah da matasa a masallatai, wannan dama ta samu ne albarkacin addinin Allah, makarantar Ahlul Baiti (AS) da Jamhuriyar Musulunci ga matasa."
Limamin Juma'ar na Qom yana ishara da haihuwar Imam Baqir (AS) ya bayyana cewa: "Duniya tana kishirwar koyarwar Imam Baqir (AS). Babbar matsalar duniya ita ce rashi ko nisantar al'ummar dan Adam daga mutane irin su Imam Baqir (AS) wadanda suka karbi ilimi kai tsaye daga wurin Allah."


Matakai Uku na Ayyukan Imamai (A.S) Domin Musulunci
Ya ƙara da cewa: "Rayuwar A'imma (A.S) ta kasu kashi uku. Kashi na farko shi ne kare Musulunci daga cutarwar karkacewa; irin karkacewar da ta faru bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W). Ga A'imma (A.S), babban abu shi ne kiyaye ingantaccen Musulunci. Wannan mataki ya fara ne daga Imam Ali (A.S) da Hazrat Zahra (S.A), kuma ya ci gaba har zuwa zamanin Imam Sajjad (A.S).
Ya bayyana cewa: "Bushara (Tabshir) da gargaɗi (Inzar) su ne sauran matsayin da aka ambata a wannan aya ga Manzo (S.A.W.A). Wato Manzo (S.A.W.A) yana nuna wa mutane hanya madaidaiciya da kuma hanyar ɓata. Idan mutane suka ga hanya amma ba su ga rami ba, akwai yiwuwar su faɗa. Idan Manzo ya nuna hanyar ɓata kawai hakan bai wadatar ba, domin idan aka hana mutum bin wata hanya, zai tambayi wace hanya zan bi? Shi ya sa dole ne a nuna hanya da rami tare."
Ya ce: "Mutane sun fi buƙatar a nuna musu rami (hanyar ɓata) fiye da nuna musu hanya, domin mutum yana bin hanya madaidaiciya bisa dabi'arsa (fiɗra), amma dole ne a nuna masa ɓarna da haɗari. Don haka a kan tituna, ana buƙatar allon gargaɗi fiye da allon nuna hanya. Shi ya sa a cikin Alkur'ani aka yi nuni da matsayin Manzo na mai gargaɗi (Munzir) kamar a Suratur Ra'ad aya ta 7 "Lallai kai mai gargaɗi ne kawai", amma koyaushe ana ambaton bushara tare da gargaɗi, domin al'umma sun fi buƙatar gargaɗi fiye da bushara."
Limamin Juma'ar na Qom ya ci gaba da cewa: "Mataki na biyu shi ne samar da tsari na musamman dalla-dalla ga mabiya (Shi'a). Dole ne a zana taswirar hanya ga Musulunci yadda za a yi amfani da ita tsawon zamani da tsararraki. Wannan mataki ya fara ne daga zamanin Imam Baqir (A.S), ya kai kololuwa a zamanin Imam Sadiq (A.S) kuma ya ci gaba har zuwa lokacin Imam Rida (A.S). A waɗannan kwanaki, an fassara kuma an bayyana ingantaccen Musulunci yadda ya kamata."
Ya bayyana cewa: "Mataki na uku shi ne shirye-shiryen karɓar ragamar gwamnati, wanda ya fara tun daga zamanin imamanci da jagorancin Imam Rida (A.S). A wannan mataki, mabiya sun kai matsayin da ya kusantar da su ga karɓar ragamar mulki."
Shugaban Haramin Hazrat Fatima Ma'asuma (S.A) ya tunatar da cewa: "Imam Baqir (A.S) lokacin da ya kai matsayin imamanci, ya ɗauki nauyin samar da tsari ga mazhabar Shi'a, wanda hakan ya gudana ta hanyar bayani, yaɗa Musulunci sosai, da kuma tarbiyyar ɗalibai waɗanda za su iya isar da wannan tsari ga wasu. Dole ne a bayyana waɗannan matakai, domin "Jihadul Tabyin" (gwagwarmayar bayani) wanda Jagora ya jaddada ya haɗa da wannan al'amari."
Ya yi nuni da shahadar Imam Hadi (A.S) inda ya ce: "Imam Hadi ya kasance a kurkukun Samarra, kuma ya yi shahada a hannun ɗaya daga cikin mafi munanan azzalumai da suka ƙwace mulkin Ahlul Baiti (A.S), wato Mutawakkil al-Abbasi. Ayyukan da ya ɗauka a lokacin imamancinsa ya gudanar da su ba tare da tsayawa ba. Bayan shahadar Imam Rida (A.S), yanayi ya yi tsanani sosai kuma rigima ta ƙaru a tsakanin waɗanda suka ƙwace haƙƙin Ahlul Baiti (A.S). A cikin sarakunan Abbasiyawa, Mutawakkil yana da hali na daban; zaluncinsa, tsananinsa, iskancinsa, da ƙiyayyarsa ga Hazrat Ali (A.S) sun mayar da yanayin zuwa lokaci mai sarkakiya."
Ya bayyana cewa: "Imam Hadi (A.S) baya ga cewa yana rayuwa ne a karkashin sa ido a Samarra, ya kuma kasance yana ruguza farfagandar ma'aikatan Abbasiyawa. Ya tsara, ya tabbatar, kuma ya ƙarfafa hanyoyin sadarwa na wakilci (Wikala) fiye da baya. Ta hanyar yaɗa koyarwar Shi'a ta hanyar wasiƙu, ya shirya mabiya ga yanayin da ke zuwa a nan gaba."
Limamin Juma'ar na Qom ya tunatar da cewa: "Yanzu da ƙasa ke fuskantar ni'imar ruwan sama na Ubangiji, dole ne a tuna da tasirin addu'a da yin sallar neman ruwa a duk faɗin ƙasa, kuma yayin da watan Rajab ke gabatowa, mu daraja wannan haɗi na ruhaniya da na sama da Allah, mu gudanar da shi a matsayin godiyar samun ruwan sama ta hanyar addu'a da salla."
Ya yi nuni da haihuwar Annabi Isah (A.S) inda ya ce: "Ɗaya daga cikin jarabawar Hazrat Isah (A.S) ita ce arangama da Yahudawa kafirai, waɗanda a yau ma dukan duniya tana fama da waɗannan sahyoniyawa masu wuce gona da iri da kisan yara. Kiristocin duniya dole ne su raba layinsu da tafarkinsu da waɗannan Yahudawa masu kisan mutane."


Ayyuka Uku na Manzo (S.A.W.A) a Cikin Suratul Fath
Ayatullah Sa'idi a huɗubar farko ya bayyana cewa: "Imam Ali (A.S) wajen siffanta masu tsoron Allah ya ce: "Suna runtse idanunsu ga abin da Allah ya haramta musu." Wannan magana tana nufin rashin kallon haram da rashin sha'awar haram. Mutum idan ya ga abu, to zai ji sha'awarsa."
Ya yi nuni da aya ta 8 a cikin Suratul Fath: "Lallai Mu mun aike ka ka zama shaida, kuma mai bayar da bushara, kuma mai gargaɗi," inda ya bayyana cewa: Sulhun Hudaibiyya ya fuskanci suka daga wasu Musulmai, jimillar waɗannan abubuwan ta sanya Allah ya jaddada matsayin Manzo (S.A.W.A), shi ya sa aka saukar da wannan aya.
Limamin Juma'ar na Qom ya ci gaba da cewa: "Allah a wannan aya ya bayyana matsayi uku ga Manzo (S.A.W.A). Allah ya sanya Manzo (S.A.W.A) ya zama shaida ga al'umma, wanda a duniya yake ɗaukar shaidar, a lahira kuma yake bayar da shaidar. Wato Manzo yana nan, yana kallo, kuma yana lura da ayyukan al'umma."
Ya ƙara da cewa: "Bayan Manzo (S.A.W.A) ma, Imami Ma'asumi yana da wannan matsayi. Matsayin Imami ba shugabanci da mulki kawai ba ne ga al'umma wanda idan an ƙwace mulkin sai ya zama ba shi da sauran aiki ko matsayi, a'a, su shaidu ne ga al'umma kuma wannan matsayi da aiki ba abin da za a iya ƙwacewa ba ne."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha