A cewar sashin kasa da kasa na Ofishin Yada Labaran Hauza, an gudanar da taron rufe wannan gasa ne a yammacin ranar Litinin, 5 ga watan Janairu, shekarar 2026 (wanda ya yi daidai da 15 ga watan Rajab, 1447), a ofishin karamin jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Karbala.
A wurin taron, wanda ya samu halartar Hujjatul Islam Wal-Muslimin Imanipur, shugaban kungiyar al'adu da alakar Musulunci, tare da gungun jami'ai, malamai, masana, da kwararrun fannin fasaha da kafafen yada labarai daga kasashen Iraq, Iran, da sauran sassan duniya, an karrama wadanda suka lashe kyaututtuka na wannan shekara.
Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini, wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a kasar Iraq, yayin da yake mika ta'aziyyar kwanakin wafatin Sayyida Zainab (AS) a wurin taron, ya bayyana cewa: "Dole ne mu koyi riko da 'Wilayah' daga wajen Sayyidah Zainab (AS)."
Ya kuma bayyana cewa wannan kyauta ta Arba’in ta duniya wani gagarumin mataki ne mai daraja wajen gabatar da tattakin Arba’in ga mutanen duniya ta hanyar amfani da yaren fasaha da kafafen yada labarai.
Your Comment