Monday 5 January 2026 - 13:47
Wilayar Imam Ali (AS) Ita Ce Ginshikin Shiriya Da Nasarar Al’ummar Musulmi

Hauza/ Hujjatul Islam Wal Muslimin Kashani ya jaddada matsayin Wilayar Alawiyya, inda ya bayyana cewa: Yin koyi da tarihin rayuwa da shiriyar Sarkin Muminai (AS) shi ne babban ginshikin samun farin cikin duniya da lahira ga al’ummar Musulmi.

Bisa rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza daga birnin Mashhad, Hujjatul Islam Hamid Kashani, masanin addini, a yau Asabar 03 ga Janairu (13 ga Rajab), a yayin bikin taya murnar zagayowar ranar haihuwar Sarkin Muminai Imam Ali (AS) wanda aka gudanar a haramin Imam Ridha (AS) tare da halartar dubban baki da mazauna birnin, ya yi bayani kan matsayin Walayya, girman ranar Ghadir, da kuma rawar da A'imma (AS) suke takawa wajen shiryar da al’ummar Musulmi.

Hujjatul Islam Kashani ya yi ishara da wani riwaya na tarihi daga Shehu Tusi, inda ya bayyana cewa: "A shekara ta 39 bayan hijira, ranar Ghadir ta zo daidai da ranar Juma'a. Sarkin Muminai Ali (AS) ya gabatar da hudubar sallar Juma'a, bayan kammalawa sai ya gayyaci mabiya (shi'a) zuwa liyafar cin abinci a gidan dansa Imam Hasan al-Mujtaba (AS). Ta haka ne aka shimfida katon kwanon abincin murnar Ghadir na farko a hukumance ta hannun Imam Hasan (AS)." Wannan riwaya, wacce aka rubuta a cikin ayyukan Shehu Tusi, tana nuna yadda aka kiyaye tare da dorewar koyarwar Ahlul-Baiti (AS) a cikin tarihi.

Malamin ya ci gaba da cewa: "Bayan shahadar Sarkin Muminai Ali (AS), saboda matsin lamba na siyasa, mabiya (Shi'a) ba su da damar gudanar da taruka a bayyane. Sai dai da hijirar Imam Ridha (AS) zuwa yankin Khorasan, wannan tafarki ya sake rayuwa, inda gidan sayyidin ya koma cibiyar ciyarwa, karramawa, da biyan bukatun mabiya."

Wannan masani na addini, tare da dogaro da bayanan Sayyid bin Tawus a cikin littafinsa mai suna Iqbal, ya bayyana cewa: "Imam Ridha (AS) ya kasance yana ciyar da duk wanda ya shiga gidansa, yana ba shi tufafi, sannan yana biya masa bukatunsa; domin duk abin da yake da shi yana bayar da shi ne a tafarkin Wilayar Sarkin Muminai Ali (AS). Wannan dabi'a kuwa wata bayyananniyar sifa ce ta hakikanin ma'anar Wilaya."

Haka nan, ya ci gaba da ishara zuwa ga wata riwaya daga Imam Sadik (AS) game da darajar Wilaya, inda ya bayyana cewa: "Imam Sadik (AS) ya dauki Wilayar Sarkin Muminai Ali (AS) a matsayin abin da ya fi kowane irin dangantaka ta jini daraja, inda ya bayyana cewa shugaban (Maula) kowane mutum yana matsayin mahaifinsa ne. Bisa wannan dalili, Sarkin Muminai Ali (AS) shi ne uba na hakika ga al'ummar Musulmi, kuma mai taimakon dukkan muminai."

Malamin ya ci gaba da jaddada rawar da Ahlul-Baiti (AS) suke takawa wajen yin ceto, inda ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya fada cewa babu wani mumini da ba shi da wani shugaba (Wali da Maula) wanda yake taimaka masa a lokutan tsanani. Wannan gaskiya kuwa babban fata ne ga mabiya (Shi'a) a duniya da lahira."

Wannan masani na addini ya yi nuni da irin damuwa mai zurfi da Imam Sadik (AS) yake da ita game da mabiyansa, inda ya bayyana cewa: "Imam Sadik (AS) a koda yaushe yana damuwa da shiriyar mabiya da tseratar da su, har ma a kwanakin karshe na rayuwarsa mai albarka, ya kasance yana rokon Allah ceton al'umma. Ya bayyana cewa duk wanda ya ziyarci Imam Ali bin Musa al-Ridha (AS) a cikin garinsa na hijira (Mashhad), to a ranar kiyama zai samu kulawa ta musamman, kuma shi da kansa Imam Sadik (AS) zai kama hannunsa ya kai shi zuwa Aljanna."

Ya jaddada cewa: "Daga dukkan wadannan riwayoyi, ana fahimtar cewa ziyarar Imam Ridha (AS) tana isa ga mutum wajen samun rabauta da shiga Aljanna, matukar dai ziyarar ta kasance tare da kiyaye alfarma, nisantar sabon Allah, rashin take hakkin wasu, da kuma tsarkaka daga kazantar zaluntar mutane."

Ya yi ishara da Ziyaratul Ghadiriyya ta Imamu Hadi (AS) inda ya ce: "Wannan ziyara tana gabatar da cikakken hoto mai zurfi game da matsayin Sarkin Muminai Ali (AS), kuma tana nuna cewa Wilayar Imam Ali ita ce ginshikin shiriya da gaskiyar addini.

Lokacin da Imam Hadi (AS) ya siffanta Sarkin Muminai Ali (AS) a matsayin hujjar Allah ga bayinsa, a haƙiƙanin gaskiya yana zana dukkan tafarkin nasarar ɗan adam ne a cikin bin tafarkin Wilaya."

Hujjatul Islam Kashani ya kuma tunatar da babban matsayi na shahidai, musamman Shahid Haj Qasem Sulaimani da Shahid Sayyid Hassan Nasrullah, inda ya ce: "Wadannan shahidai sun ɗauki kansu a matsayin sojojin Wilaya cikin alfahari, kuma ta hanyar sadaukar da rayukansu a tafarkin Ahlul-Baiti (AS), sun samar da babban girma da daukaka ga al'ummar Musulmi."

An gudanar da bikin taya murnar zagayowar ranar haihuwar Sayyidina Ali (AS) a Haramin Imam Ridha (AS), a cikin babban zauren "Talar Ayineh" da kuma masallacin "Rawaq Imam Khomeini", tare da halartar baƙi da mazauna birnin, inda aka gabatar da rera waƙoƙin yabo, madihu, da kuma karatun addu'o'i.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha