Thursday 1 January 2026 - 23:37
Koriya ta Kudu tana shirya abincin Halal ga Masu Yawon Buɗe Ido Musulmai 

Hauza/Wani gidan abinci da yake shirya abincin halal ga musulmai ya samu karbuwa sosai da farko a tsakanin daliban da ke zaune a Koriya ta Kudu, sannan daga baya ya shahara a tsakanin masu yawon bude ido musulmai. A halin yanzu, wannan gidan abinci yana da kason kashi 70 cikin dari (70%) na jan hankalin musulmai a kasar Koriya.

A cewar rahoton rukunin fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, sakamakon karuwar tallace-tallace da Koriya ke yi domin yada al'adun kasar a fannin yawon bude ido, musulmai da dama daga sassan duniya ne ke ziyartar kasar. Wannan ya sanya aka samu karuwar gidajen abinci da wuraren shirya abincin halal ga musulmai.

Duk da haka, gidajen abinci 15 ne kacal a hukumance suka samu shaidar tabbatar da ingancin abinci na halal daga Cibiyar Musulunci ta Koriya. Gidajen abincin masu taken "Halal-Friendly" (da suka dace da musulmai) ana tallata su ga juna ta hanyar kafofin sada zumunta a tsakanin mutane da masu yawon bude ido. Wadannan gidajen abinci sun samu gurbi da kuma tasiri sosai a cikin al'ummar musulmin Koriya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha