A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Jawad Marwi, mataimaki na biyu na babban zauren gudanarwar makarantun addini (Hauza), a karshen karatunsa na ranar Litinin, 1 ga watan Rajab 1447 (daidai da 22 ga Disamba, 2025), ya bayyana matsayi da muhimmancin wannan babban wata wanda sharhinsa zaku karanta kamar haka:
Bayanin Ayatullah Marwi:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
A yau, albarkacin shiga watan Rajab, zan bayyana wasu nukododi guda biyu:
Da farko, ina taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Baqir (A.S).
Abokai ne suka dage kan cewa lallai in fadi wata magana, domin ni kaina ba ni da sha'awar cinye lokacinku. Dalilin kuwa shi ne, idan mutum ya kasance mai aikata abin da yake fada ne maganarsa take tasiri, in ba haka ba ba za ta yi tasiri ba. Ni kuma galibi ina ganin kaina a rukunin na biyu, shi ya sa nake ganin yiwuwar yin tasirin maganata kadan ne. Amma zan fadi hakan ne saboda abin da aka ruwaito daga Sarkin Muminai Ali (A.S) cewa: "Yin tunani a kan alheri yana kira zuwa gare shi."
Idan har mun fahimci ma’anar hadisin daidai, to watakila manufar ita ce: samar da shimfidar tunani a kan alheri zai kai mutum ga aikata alherin.
Saboda haka, zan fadi hakan ne domin cewa isar da kalmar alheri ga wasu na iya zama sanadin samun alherin ga shi kansa mai fadar. Watan Rajab wata ne mai girma kwarai da gaske, wanda zai iya zama sanadin sauyi a aikace a cikin salon rayuwar dan Adam.
Nukuda ta Farko
Wani lokaci nakan bayyana hakan da cewa: Watan Rajab yana da matsayi na kashin kansa, sannan kuma mataki ne na kaiwa ga wani matsayi.
Akwai wasu ruwayoyi da suka zo game da watan Rajab wadanda wasu daga cikin kalaman da ke cikinsu ba su zo ko da a kan watan Ramadan ba. A cikin wani Hadisul Ƙudsi, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: "Na sanya shi (watan Rajab) ya zama igiya a tsakanina da bayina, duk wanda ya yi ruko da ita, zai sadu da Ni."
Idan bawa yana son ya kai ga matsayin saduwa da Allah, to ya mayar da hankali a watan Rajab.
Yawancin manyan malamai sukan sanya jigon lamuransu da tunaninsu mafi muhimmanci a cikin wasiyyoyinsu.
Idan kuka duba wasiyyar Marigayi Sayyid Ali Qadhi da sauran manyan malamai, za ku ga yadda suke kwadaitar da masu sauraronsu game da yadda za su shiga watan Rajab. Wannan yana nuna girman muhimmancin wannan wata.
Muna da tsananin bukatar sake gina ruhinmu da tarbiyyarmu. Wani lokaci ana fahimta daga ruwayoyi cewa: duk yadda iliminmu, shekarunmu, da matsayinmu suka karu, muna kara fuskantar hadari ne; sai dai mu a rayuwarmu akasin haka muke yi.
A farkon karatunmu na addini (dalibci), wane irin ruhi da niyya muke da su? Wadanne tunani da manufofi muke da su? Idan mutum ya ziyarci dakin kwanan matasan dalibai, yakan ji dadin yadda ake baje littattafai, kuma tare da hakan suna neman al’amuran ruhaniya.
Amma me yake faruwa ne idan matsayi ya karu, sai kaga kamar muna kaurace wa al’amuran ruhaniya? Dan Adam yana tsufa, amma wasu halaye guda biyu suna kara zama matasa (karfi) a cikinsa: Kwadayi (Hirs) da tsawon buri (Tulul Amal). Ma’asumi yana cewa duk shekaru suka karu, wadannan halaye guda biyu suna kara ruruwa a cikin ran mutum; kwadayi da tsawon buri, wadanda su ne tushen dukkan matsaloli.
Dole ne mu nemi sauyi a cikin wannan dama ta watan Rajab.
Dan Marigayi Allamah Tabataba’i yana bayar da labarin cewa: Marigayi Allamah yakan kwashe sa’a guda yana kuka, duk lokacin da muka dube shi, sai mu ga yana karanta wannan baitin wakar yana kuka:
"Ayari (na matafiya) ya wuce, kai kuma kana cikin barci..."
Shin mun taba samun mintuna goma muna tunani game da kanmu?
Mu samar wa kanmu sauyi a cikin watan Rajab; mu samar da damar yin ibadar dare (Tahajjud). Ni kaina da nake magana, hannuna fanko yake, ban sani ba ko fadin wadannan maganganun yana da amfani ko a'a. Shin a cikin wadannan dogayen darare, mutum ba zai iya tashi mintuna 45 kafin kiran sallar asuba ba don ya gyara zuciyarsa?
Malamai na baya sun kasance suna cewa idan wasu malaman tarbiyya a garin Najaf suka yi magana kan sallar dare, dalibai sukan tambayi juna cewa: "Waye sallar dare ta kubuce mawa ne har malamin nan yake magana kan muhimmancinta?" Ma'ana, yin sallar dare ya kasance daya daga cikin abubuwan da babu shakka kowane dalibi yake yi, don haka ba ya bukatar tunatarwa.
Nuƙuda ta Biyu:
Mu mayar da watan Rajab ya zama mafari na kara kusanci da addu’o’in Iyalan Gidan Manzo (A.S); da wane bakin ne kuma zamu iya bayyana cewa littafin Sahifa Sajjadiyya ya kasance abin wulakantawa kuma bako (marar masoya) a tsakaninmu?
Marigayi Agha Jamal Gulpayegani, wanda dalibi ne mai kwazo na Marigayi Na’ini, har ma wani lokacin yakan taimaki malamin nasa (Marigayi Na’ini) a al'amuran ruhaniya; lokacin da ya kai shekaru casa'in (90), dukkan jikinsa ya kasance cikin ciwo saboda ciwon kwanciya (bedsores), wanda yake daya daga cikin mafi radadin ciwo. Wannan lamari ya zama sananne a garin Najaf, har malamai ke cewa: "Muje mu ga yadda yake da natsuwa domin mu dauki darasi."
Sun ga yana da wata irin natsuwa ta musamman, sai suka tambaye shi: "Duk da wannan wahala da radadi, daga ina wannan natsuwar take?" Yana da littafin Sahifa Sajjadiyya a gefensa, sai ya fada har sau uku cewa: "Daga wannan ne."
An fada cewa a gefen karatunsa na ilimi, koyaushe yana da littafin Sahifa Sajjadiyya wanda yake karantawa kadan-kadan, lokacin idan ya karanta littattafansa kadan sai ya karanta addu'o'in da ke cikinsa.
To yanzu, shin akwai littafin Sahifa Sajjadiyya a gidan dalibi? Shin muna da masaniya a kansa?
Idan muka mayar da watan Rajab ya zama matakala da hanyar kaiwa ga wannan (karatun Sahifa), to daya ne daga cikin abubuwan da za su kai mu ga kamala; mu yi kokari mu lizimci hakan a wannan wata.
Akwai wasu bayanan kuma, idan akwai tsawon rai da taufiki, zan bayyana su idan kwanakin Ayyamul Baidh (13, 14, da 15 ga wata) sun kusato.
Ina rokon Allah ya ba mu duka taufikin amfana da alheran wannan wata, kuma mu rika yi wa juna addu'a.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammad da Alayensa tsarkaka.
Your Comment