A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Muhammad Gharavi, a wajen taron karrama fitattun masu bincike da kaddamar da ayyukan ilimi na "Cibiyar Koli ta Fikihu da Ilimin Musulunci", ya yi ishara da shahararren hadisin nan na "Unwan al-Basri" daga Imam Sadiq (A.S). Ya bayyana wannan hadisi a matsayin cikakken kundin tsarin tarbiyyar ilimi da ta ruhi, inda ya ce:
"Unwan al-Basri wani tsoho ne da ya kwashe shekaru yana kai-komo wajen Malik bin Anas, kuma tunaninsa ya kasance karkashin tasirin mazhabobin fikihu na wancan lokacin. Bayan isowar Imam Sadiq (A.S) garin Madina, ya yanke shawarar amfana da ilimin Imam kamar yadda ya amfana da na Malik. Amma a farkon lamari, Imam bai karbe shi ba. Wannan mataki na Imam yana nuna cewa isar da ilimin gaskiya yana bukatar shiri na zuciya da kuma tsari na musamman; har Imam ma'asumi ba ya bayar da ilimi ba tare da an samar da yanayin da ya dace ba."
Ya kara da cewa: "Bayan wannan haduwa, Unwan al-Basri ya fuskanci sauyi a cikin ransa; ya tafi ziyarar Annabi (S.A.W.A), ya yi sallah, ya dukufa ga addu'a, kuma ya nisanci sauran majalisu na wani lokaci, har sai da ya koma kofar gidan Imam Sadiq (A.S) da tsananin shauki. Bayan Imam ya karbe shi, ya bayyana masa gaskiyar ilimi da cewa: Ilimi ba wai kawai koyon abubuwa da tara bayanai ba ne, face wani haske ne da Allah yake sanyawa a zuciyar wanda nufinsa ya karkata zuwa ga Allah."
Yaushe ake samun Ilimi na Gaskiya?!
Yayin da yake jaddada cewa wannan bayani ba yana nufin watsi da kokarin neman ilimi ba ne, ya kara da cewa: "Imam Sadiq (A.S) ya bayyana cewa ilimi na gaske yana samuwa ne lokacin da mutum ya tabbatar da gaskiyar bautar Allah (ubudiyya) a kan kansa. Wannan bautar tana da ginshikai bayyanannu:
* Na farko: Mutum kada ya dauki kansa a matsayin mai mallakar duk abin da yake da shi, face ya dauki komai a matsayin amanar Allah.
* Na biyu: Kada ya dauka cewa yana da ikon tafiyar da al'amuransa shi kadai; ya sani cewa koda yake wajibi ne a kansa ya yi kokari ya bi hanyoyin da suka dace, amma Allah shi ne hakikanin mai tsara komai.
* Na uku: Dukkan shagaltuwar mutum ta kasance akan aikata umarnin Allah da nisantar haramun dinSa, ba wai domin daukaka kai da nuna nasarorin kansa ba."
Wannan malami na karatun Darsul Kharij ya bayyana cewa: "Idan mutum ya kai wannan matakin, ba zai fada cikin tarkon alfahari da ilimi, nuna kai, ko gasar neman daukaka a gaban mutane ba, sai dai zai dauki dukkan nasarorinsa a matsayin kyauta daga Allah. Irin wannan mahangar tana sa duniya ta zama masa mai sauki; ba wai yana nufin kwadayin duniya ba, a'a, yana nufin cewa duniya wajen jarabawa ce, ba filin nuna isa da takama ba."
Wata Masiba da ke Jiran Masu Binciken Addini
Ayatullah Gharavi, yayin da yake ishara zuwa ga ci gaban hadisin, ya bayyana cewa mataki na farko na tafiya zuwa ga Allah shi ne taƙawa. Ya ce: "Alkur'ani mai girma ya bayyana sarai cewa gidan lahira na wadanda ba sa neman daukaka ko barna a bayan kasa ne. Daukaka ba koyaushe take nufin zalunci a bayyane ba; wani lokacin daukaka tana bayyana ne ta hanyar matsayin ilimi, shahara, ko jin cewa mutum ya fi wasu tunani, kuma wannan al'amari na iya janye mai binciken addini daga hanya madaidaiciya."
Daga nan ya koma ga wasu shawarwari na dabi'un kwarai daga Imam Sadiq (A.S) game da hakuri da mu'amala da mutane, inda ya kara da cewa: "Imam yana cewa idan wani ya tunzura ku ko ya yi muku barazana, ya kamata ku kasance masu iko da kanku har ku guji mayar da martani. Idan wani ya jingina muku wani aibi, idan gaskiya ne to ku nemi gafarar Allah, idan kuma karya ne to ku nemi gafara ga wanda ya fadi maganar. Wannan hali shi ne alamun balagar ilimi da tarbiyya, kuma ga ma'abotan ilimi, hakan ya zama dole ne ma fiye da kowa."
Bukatar Guje wa Gaggawa Wajen Fatawa da Bayyana Ra'ayi
Memba a kungiyar malaman makarantar hauza ta Qum, a wani bangare na jawabin nasa, ya yi gargadi game da gaggawa wajen bayar da fatawa da bayyana ra'ayi na ilimi, yana mai cewa: "Imam Sadiq (A.S) ya jaddada cewa ku ji tsoron bayar da fatawa kamar yadda mutum yake tsoron zaki mai ruri; domin fatawa na iya sauya makomar addinin mutane. Bai kamata malami, domin neman jan hankali, ko sabuntawa ta nuna kai, ko kuma domin faranta wa wani rai ba, ya fadi maganar da za ta jawo masa nauyin shari'a da na lahira, wadda za ta sa ya zama 'gadon da wasu za su bi ta kansa zuwa wutar Jahannama'."
Yana mai jaddada bukatar tawali'u na ilimi, ya kara da cewa: "Mai bincike kada ya nuna cewa ya san abin da bai sani ba, kuma kada ya yi zaton cewa ta hanyar yin wasu darussan ilimi kalilan ya kai matsayin kammala. Sadarwa da manyan malamai da amfana da gogewar malaman da suka kwashe shekaru da dama a fagen ilimi da fikihu, shi ne sharadin ci gaban ilimi na gari."
Sabunta Ilimi Ba Yana Nufin Jayayya da Magabata Cikin Gaggawa Ba
Wannan malamin na Hauza ya ci gaba da bayar da labaran manyan malaman fikihu, ciki har da marigayi Ayatullah al-Uzma al-Khoei da marigayi Na'ini, tare da ishara zuwa ga ra'ayoyin Ayatullah al-Uzma al-Sistani, inda ya jaddada muhimmancin kiyaye tsarin fikihu na gargajiya. Ya ce: "Fikihun Shi'a sakamakon wani tsarin ilimi ne mai tushe wanda ya samo asali daga ruwayoyi, kuma ba za a iya ketare mashahuran fatawowi da ijma'in malaman fikihu cikin sauki ba. Sabunta ilimi ba yana nufin yin adawa cikin gaggawa da magabata ba; kuma kwarin gwiwa na ilimi, musamman a lokacin kuruciya, idan ba a hada shi da takawa da kiyayewa ba, zai iya zama mai barna."
Ayatullah Gharavi a karshe ya nuna cewa: "A lokacin bincike, dole ne a yi hattara kada son rai, da son zuciya su yi tasiri a kan binciken. Manufar binciken addini dole ne ta kasance gano gaskiya, ba wai tabbatar da ra'ayin kashin kai ba. Ta wannan hanyar ne kawai ilimi, a matsayinsa na hasken Ubangiji, yake zama a zuciyar dan adam kuma yake samun albarka da tasiri na gaske."
Memba a Majalisar Koli ta Makarantun Addinin Musulunci (Hauza):
Kwazo a Ilimi Idan ba a Hada Shi da Taƙawa da Kiyayewa ba, Yana Haifar da Barna
Hauza/ Memba a kungiyar malaman makarantun Hauza ta Qum, yayin da yake jaddada alaka mai karfi tsakanin ilimi da bautar Allah, ya bayyana cewa: "Gaggawa wajen bayyana ra'ayi, karfin gwiwa (na wuce gona da iri) a fannin ilimi, da kuma rashin kula da tsarin fikihu na magabata, na iya karkatar da binciken addini daga hanyarsa ta kwarai."
Your Comment