Friday 5 December 2025 - 00:20
Kiyaye Haɗin Kai, Shi Ne Al'amari Mafi Muhimmanci a Yau a Jamhuriyar Musulunci ta Iran / Masallacin Jamkaran Ya Kasance  Tsalkiyar Muhimman Abubuwan da Suka Faru a Lokacin Yaƙin Kwanaki 12.

Hauza/Shugaban Gudanarwar Masallacin Jamkaran Mai Tsarki ya ce: A yau, ba mu da wani al'amari mafi mahimmanci fiye da kiyayewa, dawwamar, da ƙarfafa haɗin kai a cikin al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma waɗannan tsarkakkun wuraren suna taka rawa kai tsaye da kuma muhimmanci sosai a wannan hanya.

A cewar rahoton ofishin yada labaran Hauza, Hujjatul Islam Sayyid Ali Akbar Ajaq-Nezhad, Shugaban Gudanarwar Masallacin Jamkaran, a yau a yayin taron Wurare Masu Tsarki na Jamhuriyar Musulunci ta Iran na takwas wanda aka gudanar a Masallacin Jamkaran, ya bayyana cewa: Wuraren masu tsarki suna taka rawa ta musamman wajen samar da haɗin kan al'umma, kuma hadin kan da aka samu a tsakanin wuraren masu tsarki a cikin waɗannan tarurrukan, za su yi tasiri kai tsaye kan ƙarfafa haɗin kan al'umma a Iran.

Ya kara da cewa: Abubuwa da dama sun samar da kaƙƙarfan haɗin kai bayan yaƙi, wanda a ciki, rawar haɓakar ruhi ta yi fice; haɓakar ruhin da muhimmin sashin sa ya samo asali ne daga ziyarar mutane wurare masu tsarki. Tasirin ayyukan wuraren masu tsarki a lokacin yaƙi da rawar da suka taka ya kasance na musamman a gaban maƙiyan Musulunci, kuma ya sake nuna ƙarfin ruhi, zamantakewa da al'adu na tsarkakan wuraren.

Hujjatul Islam Ajaq-Nezhad ya jaddada cewa: Masallacin Jamkaran bai kasance a gefe ba lokacin kariya mai tsarki na kwanaki 12 ba kawai, ya kasance ne a tsakiyar mahimmin abubuwan da suka faru. Koda dai, wannan kasancewar baya nufin wannan wurin tsattsarka ya zama cibiyar soja ba ne; amma nan ne cibiyar farko ta samar da nutsuwa, haɓakar ruhi, sanin abokan gaba, da tallafin ruhi ga mayaƙa da mutanen Iran a fagen duniya a kan gwamnatocin Isra'ila da Amurka.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha