Tuesday 2 December 2025 - 22:16
Tasirin Salati Wajen Biyan Bukatu a Bisa Mahangar Ayatullah Al-Uzma Jawadi Amuli

Hauza/ Ayatullah Jawadi Amuli ya ce: Salati da ladansa na daga cikin mafi kyawun alkhairai da lada.

A cikin rahoton ofishin dillancin labaran Hauza, Ayatullah Jawadi Amuli a cikin jawabinsa game da batun "Salati, Zikiri mai tarin albarka, " ya bayyana cewa:

Salati da ladansa na daga cikin mafi kyawun alkhairai da kuma lada. Imam Sadiq (A.S) ya ce: "Idan ka ambaci sunan Annabi (S.A.W.W.), ka yawaita salati. Domin wanda ya yi salati guda ɗaya ga Annabi (S.A.W.W), sahu dubu na mala'iku za su yi masa salati dubu, kuma duk abin da Allah Ya halitta suna yi masa salati. Kuma wanda bai sha'awar yin salati ga Annabi (S.A.W.W), shi jahili ne, mai girman kai, kuma Allah da ManzonSa da Ahlul Bait (A.S.) suna neman nisanci daga gare shi."

Ladabin addu'a da roko shi ne a fara da zikiri da godiya da yabo ga Allah mai tsarki, sannan a yi salati ga Ahlul Bait (A.S) kafin a gabatar da bukatar. Ba tare da wannan salatin ba, addu'a ba za ta amsu ba. Kuma idan wani abu ya samu wani ba tare da yin salati ga Annabi da Ahlul Bait (S.A) ba, jarrabawa ce; ba rahama da amsa addu'a ba. Kamar yadda Imam Sadiq (A.S) ya ce: "Addu'a za ta ci gaba da kasancewa a katange har sai an yi salati ga Muhammad da Ahlul Baitinsa." Saboda haka, Amirul Muminin Ali (A.S) ya ce: "A duk lokacin da kuke neman biyan wata bukata daga rahamar Allah, ku fara da yin salati ga Annabi (S.A.W.W)". Imam Sajjad (A.S) ma a cikin addu'o'in Sahifah Sajjadiyah yana koya wa masu yin addu'a wannan ladabi.

Sirrin wannan ma'anar, kamar yadda Malami mai hikima Allama Tabataba'i (R) ya ke faɗi a wani darasinsa, shi ne cewa mutum yayin yin salati ga Annabi da Ahlul Bait (A.S), yana neman rahama ga wannan dangi daga Allah Mai Tsarki, kuma wannan addu'a ta amsu. Sa'an nan kuma idan rahamar Allah ta iske su, za ta isa ga dukkan Shi'arsu, wanda mai addu'a yana cikinsu. Ta haka ne, a cikin inuwar rahamar Allah kuma saboda albarkar waɗannan mawadata masu haske, bukatarsa za ta biya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha