A cikin rahoton sashen fassara na ofishin dillancin labaran Hauza, Hujjatul Islam Abdulmajid Hakimullahiy, wakilin babban jagoran juyin juya halin Musulunci a Indiya, a cikin tarin malamai da mabiya a masallacin Ja'fariya na birnin Ranci na Indiya, ya jaddada wajibcin fahimtar ainihin addini a duniyar yau, ya bayyana cewa: Kasancewa Shi'a abin alfahari ne a gare mu; domin wannan mazhabar ta ginu ne a kan hujjoji na hankali, neman adalci da kuma kyawawan ɗabi'u.
Ya ci gaba da jawabinsa tare da nuni ga matsayin yin amfani da hankali a cikin ilimin Ahlul Bait (A.S), ya kara da cewa: Karɓar addini bisa tunani, fahimta da zurfafa tunani daga cikin muhimman siffofi ne na mazhabar Shi'a. A cikin koyarwarmu, ba kawai tunani da yin tambaya ba ne aka hana, a'a, an ƙarfafa su ne. Neman adalci kuma, shi ne tushen koyarwar Shi'a.
Wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da bayanin halayyar Amirul Muminai Imam Ali (A.S), ya ce: Wannan babban Imami bai taɓa yarda da zalunci da rashin adalci ba, saboda wata fa'ida na kashin kai ko kuma wata manufa ta wucin gadi. Bin Ahlul Bait (A.S) ba kawai alaƙa ta tarihi ba ce; a'a, hanya ce ta kaiwa ga ilimi, taƙawa da kuma shiriya ta gaskiya.
Hujjatul Islam Hakimullahi ya kuma yi nuni ga dawwamammen saƙon Ashura, ya nuna cewa: Karbala tana koya mana mu tsaya tsayin daka da juriya a gaban zalunci da karkata, kuma kada mu ja da baya a hanya ta gaskiya. Wannan makaranta, makarantar gina mutum ce kuma al'ummar yau sun fi kowane lokaci bukatar nusarwa.
A wani ɓangare na jawabinsa tare da bayyana ainihin abubuwan da ke cikin akidun Shi'a, ya bayyana cewa sanin Shi'a na gaskiya ya dogara ne akan manyan ginshiƙai guda uku:
1. Ƙarfin Akida:
Tsayayyen imani da Allah(S.W.T), da Manzon Musulunci (S.A.W), da Ahlul Bait (A.S), da tashin alkiyama da kuma adalcin Allah, su ne farkon kuma mafi mahimmanci ginshiƙin addini a Shi'a. Kuma mazhabar Ahlul Bait (A.S) ta ginu ne akan ilimi da akida bayyananna, kuma idan wannan tushe ya raunana, zasu shafi sauran bangarorin addini.
2. Kyawawan ɗabi'u da Halaye:
Wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci yayin nuni ga matsayin ɗabi'u a Shi'a ya ce: Gaskiya, aminci, tsaftar zuciya, yin hidima ga mutane da kuma gaskiya a cikin magana na daga cikin alamomin dan Shi'a na gaskiya. Babu wata al'umma da za ta iya dawwama ba tare da kyawawan ɗabi'u ba, kuma kyawawan ɗabi'u, su ne mafi girman al'amarin mabiyan Ahlul Bait (A.S).
3. Haɗin Kan Al'umma da Addinai:
Alaka mai tasiri da masallaci, Hussainiya da cibiyoyin addini, halarta tarukan addini, da kuma mai da hankali sosai ga tarbiyyar tsatso masu tasowa, shine ɓangare na uku na tushen Shi'a. Al'ummar da ba ta da alaƙa da cibiyoyin addininta, ko ba dade ko ba jima za ta fuskanci rabuwar al'adu.
Ya ci gaba da jawabinsa tare da nuni ga ƙalubalen zamanin yau, musamman a fagen al'adu da ainihin addini na matasa, ya nuna cewa: A yau ana ƙoƙarin nisantar da matasan wannan ƙarni daga sanin akidu da ƙimar addini. Idan wata al'umma ta rasa tushenta, to makomarta za ta zama fanko kuma marar ruhi. Saboda haka dole ne mu kasance masu wayo fiye da kowane lokaci kuma mu yi taka tsantsan don kiyaye ainihin addini da al'adu.
Your Comment