Saturday 29 November 2025 - 13:26
Ayatullah al-Uzma Na'ini injiniyan ilimin 'Usul' ne kuma wanda ya kafa sabon tsarin sanin bincike

Hauza/ Malami daga Hauzar Najaf ya ce: Na'ini ya kafa ma'auni, ƙa'ida da tsari na musamman ga kowane batun ilimin Usul, kuma ya gudanar da bincike kamar injiniya, tun daga farko har zuwa ƙarshe, cikin tsari.

A cewar wakilin ofishin dillancin labaran Hauza daga ƙasar Iraki, Ayatullah Sayyid Munir Khabbaz, ɗaya daga cikin manyan malamai a hauzar Najaf, ya gabatar da cikakken jawabi na kimiyya a babban taron kasa da kasa kan marigayi Ayatullah al-Uzma Muhakkik Na'ini (Q.S), wanda aka gudanar a birin Najaf mai alfarma. Babban abin da ya mai da hankali a kansa shi ne bangaren shaksiyyar Mahaƙƙiƙ Na'ini kan muhimman abubuwan da suka shafi fikihu da Usul.

A farkon jawabinsa, ya yi nuni ga matsayin Na'ini musamman a ilimin usul ya kira shi da "Injiniyan Ilimin Usul"; wato laƙabin da a cewar wannan malamin hauza, shi ne mafi dacewa da shi.

Na'ini; Injiniyan Ilimin Usul kuma Wanda Ya Kafa Sabon Tsarin ilimin Bincike

Ayatullah Khabbaz ya ce muhimmin abu na farko da za a iya gada daga Naini shi ne "kyakkyawan tsari" wato basirarsa a kan tsara tsarin batutuwan usul tun daga muƙaddima har kai wa ga natija.

Ya jaddada cewa: "Naini ya kafa ma'auni, ƙa'ida da tsari na musamman ga kowace batun ilimin usul, kuma yana gudanar da bincike kamar injiniya, tun daga farko har zuwa ƙarshe, cikin tsari."

Malamin hauzar Najaf din ya bayyana cewa: "Misali bayyananne na wannan tsari, a cewarsa, shi ne bahasosin Na'ini game da aiwatar da 'bara'a' da 'istis'hab' a cikin risalar 'Al-Libas Al-Mashkuk'; inda ya kulla iyakokin aiwatar da asalin 'bara'a' a kan shubuha na batun da kuma batun aiwatar da 'istis'hab' ko kuma rashin aiwatar da ita, ya tsara su cikin ma'auni bayyananne. Wadannan bahasosin daga baya sun bayyana a cikin 'Ajwad At-Taqrirat' da kuma a cikin rubututtukan Shahid Sadr, ko da yake akwai bambance-bambance a cikin tahlili da bayani tsakanin manyan mutanen biyu."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha