A cikin rahoton ofishin labarai na Hawzah, Ayatollah A'rafi, Shugaban Makarantun Ilimi na Hawzah, ya tafi Iraki domin halartar taron kasa da kasa kan Mirza Al-Naeeni (RA).
Bisa ga wannan rahoton: Bangare na farko na taron kasa da kasa domin tuna Mirza Al-Naeeni an gudanar da shi ne a ranar 1 ga watan Aban 1404 (23 ga Oktoba, 2025) a birin Qum, tare da sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci mai girma ya aiko, da kuma halartar Ayatollah Ja'far Subhani daga cikin manyan maraji'ai, masana, malamai da ɗalibai na makarantun ilimi na Hawzah a makarantar Hawzar Imam Al-Kazim (AS). An ci gaba da gudanar da taron a birin Mashad mai girma.
Ana gudanar da wannan taro ne tare da haɗin gwiwar makarantun ilimi na Hawzah na Qum da na Iraki da kuma wurare masu tsarki (Haramomi masu girma). Ana ci gaba da gudanar da shi a cikin garuruwan Najaf Ashraf da Karbala a ranakun 6 da 8 ga watan Azar, inda manyan mutane daga makarantun addini na Hawza da ƙasashen Musulmi suka halarta.
Your Comment