Thursday 23 October 2025 - 18:54
Me ya sa ake kiran Allah “mafi kyan masu halitta”,  alhali kuwa babu wani mahalicci?

Hawza/ Siffanta Allah da cewa “Mafi alherin masu halitta” yana nuni da kebantuwarsa da fifikonsa na haƙiƙa a cikin yin halitta, ba samuwar wasu masu yin halitta ba.

Kamfanin dillancin labaran Hauza ya bayyana cewa, kalmar "mafi kyawun halitta" a cikin ƙur'ani mai tsarki na nuni da faffaɗan ma'anar halitta da kuma fifikon Allah a matsayinsa na mahalicci ɗaya tilo, ba wai akwai mahalitta da yawa ba.

Siffanta Allah da cewa “Mafi kyan masu halitta” ba ya nufin cewa akwai wasu masu yin halitta - ɗin banda shi. Kalmar “halitta” ba wai tana nufin ƙirƙirar wani abu daga babu ba ne, a’a, a wasu lokuta ma ana amfani da ita ta wasu ma’anoni, kamar aunawa, ginawa, da samar da sabbin siffofi ga abubuwan da suke dama akwai su.

Su Muta ne, da dabarun da Allah mai girma ya basu, suna iya canza abubuwa daban-daban; misali, za su iya yin kayan aiki daga ƙarfe da narkakken ƙarfe, ko kuma gina gine-gine masu ban sha'awa ta hanyar ma'auni daidai tacce ba kuskure. Waɗannan nau’i ne na “halitta” -suma, a fagen faɗaɗa ma’anar halitta, amma halitta ta gaskiya wadda ita ce halittar kwayoyin halitta da siffa daga babu, waɗanna da daga Allah ne kaɗa suke fitowa.

Alkur'ani mai girma ya yi bayanin hakan da ambato labarin Annabi Isa (as) cewa: "Ni ne zan halitta muku daga yumbu a cikin siffar tsuntsu, sa'an nan in hura masa a cikinsa, sai ya zama tsuntsu da iznin Allah." A nan, “halitta” na nufin ba da siffa da hura rai ga wani abu da ya riga ya kasance - akwai shi dama, ba halitta abu daga babu ba ne.

Saboda haka, idan muka kira Allah "mafi kyawun mahalitta," yana nufin cewa shi ne mafifici kuma shi kaɗai ne mahalicci na gaskiya, kuma sauran masu yin halitta kawai suna aiki ne a fagen canji da ginawa.

Don dubawa:
(1). Suratul Al-Imran, aya ta 49.
(2). Littafin Saƙon Alqur'ani, na Makarem Shirazi, Nasser, Darul Kitab Al-Islamiyya Publications, Tehran, 2007, bugu na 9, juzu'i. 2, shafi na 78.

Madogara: sahen Amsa tabayoyi akan shakku na tauhidi na Ofishin Ayatullah Makarem Shirazi

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha