Kafar Yada Labaran Hauza ta bada rahon cewa, Ranar Laraba bayan sallolin Magrib da Isha’i, 26 ga Jumada al-Thani, 1447, wanda ya yi daidai da 17 ga Disamba, 2025, Cibiyar Albasira, Sashen 'Yan'uwan Mata, Qom, karkashin jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ta shirya tare da gudanar da Mauludin shugabar mata ta Duniya da Lahira, Fatima Zahra (SA).
An fara Taron Mauludin ne da buɗe taro da addu'a, sai kuma aka yi karatun Alkur'ani Mai Girma.
Bayan haka, sai aka karanta Ziyarar Sayyida Fatima (SA).
Mallama Fatima Aminu ce ta fara gabatar da jawabi na farko, inda ta bayar da takaitaccen tarihin Ummul Hasanain (Uwar su Hasan da Husayn (As), tare da kawo wasu daga cikin kyawawan halayen wannan uwargida tamu.
A ƙarshe, ta yi kira ga 'yan'uwa, musamman Sistoci, da su yi koyi da dabi'u da tarbiyyar Sayyida Zahra (SA).
Hujjatul Islam Abdulhadi Isah Richifa, a jawabin ta'alikin da ya gabatar, ya bayyana murna ga 'yan'uwa tare da bayyana wannan babbar ni'imar da Allah (SWT) ya yi wa al'umma, sannan ya bayyana wasu matsayi da darajojin Sayyida Batula.
Hujjatul Islam Abdulhadi ya bayyana cewa: "Sayyida Zahra (SA) ita ce macen gidan Annabin wannan al'umma. Domin lokacin da Manzon Allah (SAWA) zai yi Mubahala da Kiristoci a Madina, kamar yadda ya bayyana a cikin Alkur'ani cewar Allah (SWT) ya umurci a zo da mata, Manzon Allah (SAWA) ya zo da Sayyida Fatima ne, duk da cewa akwai sauran matan Annabi.
Wannan yana nuna mana girman darajar wannan babbar uwargida.
Sheikh Abdulhadi ya ƙara da cewa: "Sayyada Zahra (SA) ta kasance 'yar gwagwarmaya ce, wacce ta zama gwarzuwa wajen kare Wilaya da Imamin zamaninta."
Saboda haka, ya yi kira ga 'yan'uwa maza da mata da su yi koyi da Sayyida Zahra wajen daƙewa a kan tafarkin gwagwarmaya da rashin tsoro.
A ƙarshe, Mallamin ya yi magana a kan wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Khumaini (QS), wanda shi ma aka haife shi a ranar da aka haifi Sayyida Zahra, wato 20 ga watan Jumada al-Thani.
A yayin taron, an gudanar da waƙoƙin yabo ga shugabar matan Duniya da Lahira. Sannan ayarin waƙa na "Abna'u Ruhullah" karkashin Cibiyar Albasira suka gabatar waƙensu a wurin.
A ƙarshe, an gudanar da kacici-kacici ga yara manyan gobe, wanda Mal. Musa Shuaibu ya jagoranta.
Bayan kammalawa, sai aka rabawa yara kyaututtuka.
A ƙarshen taron, an yanka alkaki guda biyu: ɗaya na Sayyida Zahra (AS) ɗayan kuma na ɗanta Imam Khomaini (Qs).
Bayan yanka alkakin, sai aka raba walima, sannan aka yi addu'a aka sallami mahalarta taron.
Sashen Media, na Cibiyar Albasira Qom, Harakar Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaaqub Zakzaky (H)














Your Comment