Hauza/ Hujjatul-Islam wal-Muslimin Sheikh Ali Al-Khatib, mataimakin shugaban Majalisar Ɗinbin Musulman Shi’a ta Lebanon, ya yi tsatsauran suka kan munanan hare-haren da Isra’ila ke ta maimaitawa a kan Lebanon.
A cewar Sashen Fassara na Cibiyar Labaran Hauza, Sheikh Ali Al-Khatib, mataimakin shugaban Majalisar Ɗinbin Musulman Shi’a ta Lebanon, ya fitar da sanarwa inda ya yi tsananin Allah-wadai da hare-haren da Isra’ila ke ta kaiwa kasar Lebanon ba kakkautawa.
Ya bayyana wadannan hare-hare a matsayin karya sararin ikon Lebanon, da kuma take hurumin fararen hula, lamarin da ya zama jerin manyan laifuka masu ci gaba. Daga cikin sabbin misalan wadannan laifuka har da kisan gillar da aka yi a Ainul-Hilwah da kuma harin da aka kai a At-Tayri, inda makashin Bayahuden Sahyoniya ya yi harin kwantanbauna a kan fararen hula marasa laifi, matasa, yara da kuma daliban jami’o’i da sauran makarantun ƙasa.
Sheikh Al-Khatib ya bayyana wadannan ayyukan ta’addanci da aka tsara cikin tsari a matsayin kutse kai tsaye ga Lebanon da dukan ‘yan Lebanon, wadanda ke da alhakin nuna hadin kai da tallafi ga jama’arsu da ‘yan uwansu a cikin ƙasa.
Mataimakin shugaban Majalisar Ɗinbin Musulman Shi’a ya kara da cewa: muna gabatar da wadannan laifuka dake ci gaba da afkuwa a gaban Majalisar Ɗinkin Duniya, kungiyoyin kasa da kasa, kasashe abokai da makwabta, da kuma kwamitin tsare-tsare, tare da kira gare su da su dauki matsayi mai tsauri na Allah-wadai da wadannan munanan ayyuka, su kuma dakatar da wannan kutse mara yankewa da ake yi wa jama’armu; domin ba abin yarda ba ne yara da manya fararen hula su ci gaba da zama ganima ga ta’addancin Isra’ila wanda ya yi daidai da kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza.
Ya kuma bukaci gwamnatin Lebanon da ta gudanar da aikinta na doka ta hanyar daukar nauyin dakatar da kisan ‘ya’yan al’ummar kasar. Ya ce wajibi ne gwamnati ta hanzarta daukar matakai a cikin majalisun kasa da kasa, kungiyoyin kare hakkin bil’adama da kuma ofisoshin jakaduncinta a kasashen waje domin bayyana laifukan Sahyoniya da jawo hukunta su, tare da nuna goyon baya ga wadanda abin ya rutsa da su cikin shahidai da raunana, ba tare da barin ko wace hanya don takaita wannan harin da ake kai wa Lebanon ba.
A ƙarshe, Sheikh Al-Khatib ya mika ta’aziyyarsa ta gaskiya ga iyalan shahidan, wadanda ya bayyana cewa “a wurin Ubangijinsu raye suke, suna karbar arziƙi”. Ya roki rahamar Allah a gare su, ya nema wa iyalansu haƙuri da nutsuwa, tare da roƙon gaggawar waraka ga masu fama da raunuka.
Sheikh Ali Al-Khatib.
Your Comment