Hauza/ Dandalin Albasira tare da kungozar Daliban Jamia Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaaqub Zakzaky (H) Iran ya gabatar da taron shahadar Sayyidatu Nisa'il Aalamim, Fatimatuz-Zahra a Jami'ar Shahed, Tehran.Taron ya samu albarkar jawabinsu Ummus-Shuhada, Mallama Zeenatudden Ibrahim. 

Cibiyar labaran Hauza ta labarata cewa, Dandalin Albasira tare da kungozar Daliban Jamia Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaaqub Zakzaky (H) Iran ya gabatar da taron shahadar Sayyidatu Nisa'il Aalamim, Fatimatuz-Zahra a Jami'ar Shahed, Tehran.Taron ya samu albarkar jawabinsu Ummus-Shuhada, Mallama Zeenatudden Ibrahim. wanda Tun da farko dai an fara da bude taron da karatun Alkur'ani mai tsarki, karanta ziyarar Ashura, addu'ar Tawassul , ziyarar Sayyida Zahra (SA) tare da sauran addu'o'i. Bayan kammala addu'o'in ne sai mawaka suka gabatar da waken juyayi.


A farkon jawabinta, Mallama Zeenah ta fara da bayanin shahadar Sayyida Zahra, wanda ta ce amfanin tunawa da mazlumiyar Sayyida Fatima shi ne yin koyi da ita wajen kare abin da akan sa ne abin da ya same ta ya same ta. Mallama ta kara da bayyana cewa da zai zama kawai sai mutum ya zama yayi bakin ciki da juyayin abin da ya same ta, amma kuma ya ki tsayawa don kare tafarkin abin da akan sa ne ta yi shahada to zai zama bai amfanar ba, amma kuma koda mutum bai yi taron tunawa da bakin cikin abin da ya same ta ba amma ya tsaya ƙyam domin kare tafarkin da take a kai na yin fada da zalunci yafi yayi taron amma yana goyon bayan azzalumai.


Ummus-Shuhada ta kara da cewa duk bala'o'in da al'umma suka sami kansu a ciki sakamakon abin da aka yi ne bayan wafatin (shahadar) Manzon Allah (SAWA), domin da al'umma sun bi wasiccin Manzon Rahama to da yanzu duniya ba ta cikin wadannan bala'o'in da take ciki, kuma da an samu cigaba masu tarin yawa.


Da take bayanin yadda wani Mallami a shekarun baya yana bayani akan abin da ya faru bayan wafatin Manzon Allah, yana cewa wai Sayyida ta jajirce ne saboda a bawa mijinta shugabanci, Mallama ta ce mace mumina da ta san Allah kuma ta san nauyin jagoranci ba za tayi fatan mijinta ko ita su zama shugabanni ba, saboda hakkokin da suke kansu da kuma tambayar da za a yi musu ranar Lahira. Don haka Sayyida Zahra ta jajirce ne domin umarnin da wasiccin da Annabi yayi kafin shahadarsa.


Da ta koma kan dalibai masu karatu kuwa, Mallama Zeenah ta jawo hankalinsu akan cewa su yi karatu ne da nufin taimakawa Harkar Musulunci karkashin jagorancin Imam Sayyid Zakzaky (H), ko me mutum ya ke karanta kuwa. Sannan ta jawo hankalin daliban akan yadda ake wasa da hankalin wasu daga ciki akan cewa a bi azzalumai, yanzu ba lokacin gwagwarmaya ba ne, lokacin yada Shi'anci ne, inda Mallama ta ce akwai abin mamaki akan hakan, "To menene shi'ancin idan ba fada da zalunci ba da kuma bin dokokin Allah?". Akwai abin takaici ya zama an yaudari mutum da wannan tunanin musamman wanda yake Iran, wanda sakamakon kawar da gwamnatin zalunci da kuma kafa gwamnatin Allah ne da Imam Khumaini Qs yayi ya sa har ya samu damar zuwa kasar ya ke karatu.


Mallam Zeenatudden ta kara da yin nasiha kan sallamawa dari bisa dari ga umurnin Allah (T) wanda ta ce shi ne ma'anar Musuluncin, inda zai zama mutum zai sallamawa Allah kashi casa'in da tara cikin dari (99%) sai ya zama da gangan yaki sallamawa da kashi daya, to da yayi aikin banza ne, domin shi Allah ana sallama masa dari bisa dari (100%) ne.


A karshe-kaeshen jawabinta ta tabbatar wa da yan uwa cewa Addinin nan zai tabbata a Nijeriya, kawai yan uwa su yi abin da ya hau kansu ne, dama ba su ne masu tabbatarwar ba, Allah ne zai tabbatar, don haka kowa ya sauke wazifar da take kansa. Ba wani karfi da ya isa ya hana kafuwar hakan, ba Amurka da Isra'ila da Jafan ba.


Daga karshe Mallama ta ja hankalin yanuwa akan su dage da ayyukan ibada da gyaran kai, sannan su hada da addu'ar tabbatuwa a kan addinin.
Kafin isowar Umma din Mallam Muhammad Sani Malafa da Mallam Abdullahi Ahmad Fudiyya sun gabatar da nasiha ga yan uwan.


Taron dai ya samu halartar daliban Hauza daga Qom tare da daliban Jami'o'i daban daban. Daga karshe Umma Zeenah ta rufe taron da addu'a kana aka sallami yan uwa.

Daga Media Forum, Dandalin Albasira Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), Qom

21 Jimada Awwal, 1447
11 Nuwamba, 2025

Umma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin TehanUmma Zeenah Ta gabatar da Jawabin Shahadar Sayyida Zahra (as) a Birnin Tehan

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha