Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayar da rahoton cewa, Shaheed Motahari (RA) ya yi ishara da wani batu a cikin littafinsa na Azadi Ma'anawi, wanda ke da matukar amfani ga iyayen da suka damu da yayansu su zama masallata.
Masallatan da suke rasa sallar da kansu; Wato suna kaskanta sallar (sallar asuba sai gab da fitowar rana, sallar azahar da la'asar sai gab da faduwar rana, sallar magriba da isha sai bayan awa hudu da wucewar rabin dare sannan kuma suna yin sallah cikin gaggawa) abin da tajruba ta nuna shi ne cewa yaran wadannan sam ba sa sallah!
Idan da gaske kuna son ku kasance masallata kuma 'ya'yanku su kasance masu yin Sallah, to dole ne ku girmama sallah.
Ba ina cewa ku daga murya yayin yin sallah ne ba; girmama sallah sama yake da daga murya a sallah.
Da farko dai ku zabi wurin sallah da kanka a gida (mustahabbi ne) wato ku ware wani wuri ku maida shi gun sallar ku a gida.
Idan zaku iya (kamar yadda Manzon Allah yana da dakin sallah, yana da wurin yin sallah) ku zabi wani dakin a matsayin dakin yin sallar ku.
Idan ba ku da ɗakuna da yawa, ku ware wani wurin musamman domin yin sallah.
Ku kasance kuna da sallaya mai tsafta don yin sallah, ku sanya sallaya mai tsafta a wurin da zaku tsaya domin yin sallah, ku yi burushi sannan kuma ku samu carbi don yin zikiri.
Idan zakuyi alwala kada ku yi ta facal-facal cikin gaggawa.
Madogara: Mortadha Motahhari, Azadi Ma'anawi, shafi na 89
Your Comment