A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, ma'aikatar ta bayyana cewa a wannan dare, an yi tafiya da Manzon Allah (SAWA) daga Masallacin Haram da ke Makka zuwa Masallacin Aqsa da ke Kudus (Palestine). Bayan haka, ya yi mi'iraji zuwa sammai madaukaka har zuwa Sidratul Muntaha, inda babu wani babban manzon da aka aiko ko Mala'iku na kusa da Allah da ya taba kaiwa gare shi kafin sa.
Ma'aikatar ta bayyana cewa daren Isra'i da Mi'iraji wani lokaci ne mai muhimmanci a Musulunci, domin a wannan dare ne aka wajabta salloli guda biyar a kan al'umma. Ma'aikatar ta kara da cewa mu'ujizar ta tabbata kwarai da gaske ta hanyar Alkur'ani mai girma, sunnar Annabi (SAWA), da kuma ijma'in malamai. Ta kafa hujja da ayoyin farko na Suratul Isra'i "Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bawanSa (Annabi Muhammad) daga Masallacin Haram (da ke Makka) zuwa Masallacin Aqsa (da ke Kudus), wanda muka sanya albarka a kewayensa, domin Mu nuna masa daga ayoyinMu (na mamaki). Lallai Shi (Allah) Mai ji ne, Mai gani." Sannan da kuma ayoyin Suratun Najmi "Kuma lallai ya gan shi (Mala'ika Jibrilu) a wata sauka ta daban." (Aya 13)
"A wurin Sidratul Muntaha (itacen magaryar ƙarshe)." (Aya 14)
"A wurinta (Sidratul Muntaha) akwai aljannar nan ta zama (Jannatul Ma'awa)." (Aya 15) wadanda suka yi bayanin daki-daki game da Mi'iraji.
Ma'aikatar ta fayyace cewa wannan mu'ujiza ta faru ne da jiki da kuma ruhi na Annabi (SAWA) a lokaci guda, ba wai a mafarki ba kawai.
Dangane da hadisin Anas bin Malik, an bayyana cewa Annabi (SAWA) ya hau kan Buraka. Ya daure ta a Masallacin Aqsa, ya yi sallah raka'a biyu, sannan ya haura zuwa sammai tare da Mala'ika Jibrilu (AS).
Ma'aikatar ta lissafa wasu daga cikin hikimomin wannan mu'ujiza da suka hada da nuna daukakar matsayin Annabi (SAWA) a wurin Allah, yaye bakin cikin Annabi bayan "Shekarar Bakin Ciki" (Amul Huzni), inda ya rasa baffansa Abu Talib da matarsa Sayyidah Khadija (AS), tace muminai na gaskiya daga wadanda imaninsu yake da rauni, nuna sakamakon lada da ukuba na al'umman da suka gabata, tabbatar da fifikon sakon Musulunci akan sauran sakonni da kuma shiryar da mutane ga sanin muhimmancin yin Sallah da ibada dai-dai kuma don Allah.
A ƙarshe, Ma'aikatar Waƙafin ta jaddada cewa Isra'i da Mi'iraji wata babbar mu'ujiza ce kuma maras tamka ga Musulmai, wadda ke nuna ikon Ubangiji da kuma babban falalar Allah ga Annabi (SAWA) da al'ummarsa. Mu'ujiza ce wadda ta tabbata ta hanyar Alkur'ani, Sunnah, da ijma'in Musulmai (haɗin kan malamai), kuma ana ɗaukarta a matsayin wani mataki mai muhimmanci wajen ƙarfafa harsashin addinin Musulunci."
Abin lura shi ne cewa, Ma'aikatar Waƙafi ta ƙasar Masar ta fitar da wannan sanarwa ne domin zagayowar daren Isra'i da Mi'iraji, wanda a cewar wata ruwaya ya faru ne a ranar 17 ga watan Rajab. Sauran maganganu (ra'ayoyi) game da kayyade ranar Mi'iraji su ne 17 ga watan Ramadan, shekara 12 kafin Hijira, 17 ga watan Rabi'ul Awwal kafin Hijira, 17 ga watan Rajab kafin Hijira, 17 ga watan Ramadan, shekaru 5 kafin aiko Annabi, 27 ga watan Ramadan da 9 ga watan Zul-Hajji.
Your Comment